Hawan Babbar Sallah: Masarautar Katsina Bata Yi Hawan Bariki Ba – Mai Martaba Sarki
Mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumi Kabir Usman ya bayyana cewa ba za ayi hawan bariki ba kamar yadda aka saba duk shekara ba
Sakon hakan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren masarautar Alhaji Sule Mamman Dee ya sanyawa hannu sannan akan rabawa manema labarai a Katsina.
Haka kuma Popular News Hausa cewar za a gudanarda Hawan Sallah Babba na wannan shekara wadda ake tsammanin yin ta a ranar 9th July, 2022, insha’ Allahu.
Sanarwar ta ce bayan haka, Mai-Martaba ya sake ummurtata da cewar Hawan Sallah kadai za’agudanar, ,ba za’a samu damar Hawan Bariki ba.
Don haka za’a gudanar da Sallar Idi kuma za’a gudanar da addu’oi na musamman a ko’ina cikin jihar Katsina nan domin neman zaman lafiya
Haka kuma Mai martaba Sarkin Katsina yana fatan Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya, Allah Ya zaunar da Kasar mu lafiya, amin.
