Dubbanin mabiya addinin kirista sunyi dafifi a gidan Gwamnatin jihar Bauchi Domin mika gaisuwan kirsimeti ga mai girma Gwamnan jihar Sanata Bala Abdulkadir Muhammad Kauran Bauchi
A safiyar yau Asabar 25/12 /2021 ne Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Kauran Bauchi ya karbi bakuncin mambobin kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN reshen Jihar Bauchi wadanda suka kai masa gaisuwar Kirsimeti a gidan gwamnati Bauchi.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Bala ya taya su murna sannan kuma ya bukace su da su yi amfani da lokacin kirsimeti wajen yin ayyukan alheri da kuma koyon darasu zaman lafiya da addinin ya koyar.
Gwamnan yayi kira ga kiristoci da su mika hannun ‘yan’uwantaka ta zumunci ga mabiya sauran addinai domin wanzar da zaman lafiya kamar yadda Yesu almasihu yayi umarni ga mabiyan sa.
Gwamnan ya ci gaba da yin kira ga fastoci da su maida hankali wajen yin wa’azi na zaman lafiya, gaskiya, soyayya da kuma juriya. Tsakanin mabiyan su kamar yadda yake a koyarwan addinin kirista.
Gwamnan ya jaddada bukatar fahimtar juna da mutunta juna tare da zaman lafiya a tsakanin sauran mabiya addini a fadin jihar Domin a cewar sa rungumar ka’idar zaman lafiya ne kawai zai kawo cigaba ga al’umma domin sai da zaman lafiya ake iya morar Dukkanin ayyukan cigaba da Gwamnati zata kawo ma al’umma.
Tun da farko, Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Bauchi, Rabaran Abraham ya nuna jin dadinsa ga Gwamna Bala bisa irin karimcin da yake yi wa al’ummar Kirista a jihar Bauchi.
Shugaban CAN din ya ce-: domin wanzar da zaman lafiya a jihar kungiyar ta CAN tare da hadin gwiwar majami’u sun fara gudanar da addu’o’i na musamman da nufin Ubangiji ya daurar da zaman lafiya a jihar Bauchi. Dama Nijeriya baki daya Allah ya kawo mana karshen kashe kashen da akeyi a Arewa.
Shugaban yace kiristocin jihar Bauchi za su ci gaba da sanya Gwamnatin sa cikin addu’a domin samun Nasara da ci gaba da da wanzar da ayyukan alheri ga al’ummar jihar Bauchi.
Lawal Muazu Bauchi Mai Taimakawa Gwamnan jihar Bauchi kan Sabon Kafafen Sadarwa.
25/12/2021
