September 16, 2026

Da Gaske Akwai Ajin Da Ɗaliban Aji 4 Da 5 Da 6 Suke Ɗaukar Darasi Aciki- Lawal Buhari Daura

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

An samu wata makarantar firamari a jihar Katsina da ɗalibai ‘yan aji huɗu da biyar da shida suke ɗaukar darasin karatu a cikin aji ɗaya saboda ƙarancin ajujuwa da ake fama da su.

Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya na jihar Katsina, Alhaji Lawal Buhari Daura ya tabbatar da haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a ofishin sa da ke Katsina.

Ita dai wannan makaranta tana da ɗalibai 644 sannan tana da malamai 8 biya na S-power 1 N-Power sai kuma biyar na dindindin, haka kuma ƙauyuka uku ne suke haɗa wannan makaranta da suka haɗa da Saƙe da Katakalo da kuma Ƙawari duk acikin karamar hukumar Charanci ta jihar Katsina.

Wannan dai na zuwa ne lokacin da wakilan kafafen yaɗa labarai suka kai ziyarar gani da ido a wannan makarantar firamari da ke garin Saƙe da ke cikin ƙaramar hukumar Charanci a jihar Katsina.

Kazalika ya bada amsa dangane da yadda wasu makarantu ke fuskantar barazana ɗaukewar rufe sakamakon iska da ruwan sama na damina wanda ya ce lallai gwamnati na sane kuma suna ɗaukar matakan gyara a duk fadin jihar Katsina.

” Wato duk abubuwan da aka faɗa na matsalolin da makarantun firamare ke fuskanta da gaskiya ne, amma abin ne ya yi yawa, kasan ance idan dambu ya yi yawa baya jin mai, kuma tun daga zuwa wannan gwamnati zuwa yanzu an yi ayyuka da suka haɗa da gyara da kuma gina wasu sabbin ajujuwa” inji shi.

Ya ƙara da cewa daga zuwa wannan gwamnati ta damu da yadda ta samu harka ilimi musamman na firamare da ma na sakandare wanda duk shekara sai an ba ilimi fifiko a kasafin kuɗin jihar Katsina.

Alhaji Lawal Buhari ya ce gwamnati jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari ta kashe kuɗaɗe wuri na gugar wuri har fiye da naira biliyan tara wajan gina sabbi da gyara makarantu da sanya kujerun zama a cikin shekaru bakwai.

“Tsakanin gyara da gina sabbin ajujuwa da samar da kujerun zama, fiye da makarantun 4,590,00 suka amfana daga wannan gwamnati acikin shekaru bakwai a faɗin jihar Katsina baki ɗaya.” Inji shi

Haka kuma shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ya ce idan kuma an duba waɗanda suke da matsala ya kamata a duba waɗanda aka gyara ko a gina sabbi, ya ce duk makarantu da aka gani da kalar fanti ja da bulu to wannan gwamnatin ta gyara ko ta gina.

Wasu daga cikin katarantu da suke fuskantar matsalolin sun haɗa da Saƙe a ƙaramar hukumar Charanci da Ɗaɗɗara Liman da Kwarare sauransu duk a cikin ƙaramar hukumar Jibia da kuma wasu da dama a jihar ta Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *