Rashin Tsaro A Zamfara: Yan ta’adda Sun Tada Al’ummar Mada.
Wasu ‘yan ta’adda sun mamaye al’ummar Mada dake karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Majiyoyi daga al’ummar sun ce mazauna al’ummomin dake fama da rikici sun bar al’umma sakamakon hare-haren da ake kai wa, wanda ya yi sanadin kashe-kashe da sace-sacen dabbobi.
Hare-haren na baya-bayan nan a cikin al’ummar dake fama da rikici da kauyukan dake kewaye shi ne na ranar Alhamis din da ta gabata lokacin da ‘yan ta’addan suka far wa kauyukan, tare da kai wa al’ummar yankin hari, inda suka kashe wani dan banga na yankin, tare da yin garkuwa da wasu mazauna kauyukan guda bakwai.
‘Yan ta’addan sun kuma koma unguwar Mada a ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka sake kai wani sabon hari a kan al’ummar yankin suka kashe Mutane goma sha biyu, inji majiyar Popular News Hausa ta AIT.
Mazauna yankin sun ce ‘yan ta’addan sun mamaye kauyukan ne da misalin karfe 5 na yamma, inda suka rika harbin mazauna garin, kuma suka yi garkuwa da Mutane uku.
Kauyukan da ‘yan ta’addan suka kai wa hari sun hada da Gidan Bangi da Ruwan-bore dake gundumar Mada cikin Gusau.
Rahotanni sun ce da yawa daga cikin mazauna unguwar Mada sun bar gidajensu zuwa yankin Kwatarkwashi dake karamar hukumar Bungudu a jihar.
Kuma kokarin samun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Mohammed Shehu don ya tabbatar da lamarin, ya ci tura domin bai amsa kira ko sakon waya da aka aika masa ba.
