November 18, 2026

Yan Bindiga Sun Fille Kan Tsohon Dan Majalisa A Anambra.

0

Wasu ‘yan bindiga sun fille kan wani tsohon dan majalisa a jihar Anambra dake kudu maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da marigayin mai suna Nelson Achukwu daga karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra watannin da suka gabata, inda suka zarge shi da bayar da bayanai ga hukumomin soji.

Sai dai an sake shi ne bayan wadanda suka yi garkuwa da shi sun fahimci cewa ba shi da laifi a kan zargin.

An sake yin garkuwa da Mr. Achukwu, da ke zama mai bukata ta masamman makonni uku da suka gabata daga gidansa da ke unguwar Mkpor, ina aka fille masa kai bayan iyalansa sun biya Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa ga ‘yan bindigar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar wa majiyar Popular News Hausa ta PREMIUM TIMES faruwar lamarin a yammacin Larabar nan.

Ya ce an tsinci gawar tsohon dan majalisar ne a ranar Talata tsakanin iyakar al’ummomin Uke da Ukpor da ke yankin karamar hukumar da abin ya faru.

“An tsinci gawarsa da aka yanke ma kai a bayan kogin Ulasi, inda kuma dangin sun yi gaggawar binne shi a yammacin ranar Talata saboda tuni gawar ta fara rubewa.

Kakakin ‘yan sandan ya ce ‘yan sandan ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da bincike a kan lamarin, ya kuma ba da tabbacin cewa za a zakulo wadanda suka aikata laifin.

Mr. Achukwu shi ne mamallakin fidan man Nelly Oil & Gas Filling Station da kw Utuh.

Kuma ya taɓa wakilci mazabar Nnewi ta Kudu 2 a majalisar dokokin jihar a zamanin gwamnatin tsohon gwamna Chris Ngige, wanda yanzu shi ne ministan kwadago da samar da ayyukan yi na Najeriya.

Tsaro a yankin Kudu-maso-gabashin Najeriya ya tabarbare a ‘yan kwanakin nan, inda ake samun rahotannin kai hare-hare a kusan kowace rana a fadin yankin.

Jihar Anambra ta sha fuskantar munanan hare-hare kan hukumomin tsaro, jami’an gwamnati da dai sauransu.

Harin na baya-bayan nan dai ya zo ne daidai wata daya da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Okechukwu Okoye, dan majalisa mai wakiltar mazabar Aguata 2 a majalisar dokokin jihar Anambra, sannan suka fille masa kai.

An kashe Mista Okoye ne a ranar 21 ga watan Mayu tare da mai taimaka masa, Cyril Chiegboka, kwanaki shida bayan da aka yi garkuwa da su a hanyar Aguluzigbo, a karamar hukumar Anaocha ta jihar.

Har ila yau, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Uzozie Chukwujekwu, mai ba tsohon shugaban karamar hukumar Nnewi ta Kudu shawara na musamman, sannan kuma suka harbe dansa daya tilo sa’o’i kadan bayan labarin fille kan Mr. Okoye ya fallasa.

Gwamnatin Najeriya na dai zargin haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra da laifin kai munanan hare-haren a yankin. Sai dai kungiyar ta sha musanta hannu a ciki.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *