Iyayanda Aka Sai Da Sasan jikin Ɗansu Ahmad Sun Koka Da Shari’ar Da Ake Masu A Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim.
Iyayan Ahmad Yakubu, dan shekaru tara da wasu suka yankashi suka saida sasan jikin sa ga Aminu Baba, Gusau sun koka ga yadda akewa shari’ar zagon Kasa a Gusau babban burin jihar Zamfara.
Salisu Abduraham Hafizi daya daga cikin iyayan yaran ne ya bayyana haka, a alokacin da suke mika kokensu ga ‘yan jaridu a Sakatareyar N U J dake Gusau babban birnin jihar Zamfara.
A jawabin sa Hafizi ya bayyana cewa, idan ba ku manta ba, kimanin watanni Shida da suka gabata, kunyi Hira da wasu mutane da suka tabbatar maku su suka kashe danmu Mai suna Ahmad Yakubu suka Kuma cire sassan jikin shi suka sayar ma wani Mai suna Aminu Baba Wanda shima ya tabbatar maku da hakan Kuna daukar muryar shi da Kuma hoto Mai motsi wato Bidiyo a harabar hedikwatar Yan sanda dake Anguwar gwaza Gusau.
‘Haka zalika rundunar ‘Yan sandan ta gurfanar da Wanda ake zargin a gaban kotun Chif Majistare wadda Maishara’a Sa’adu Gurbin Bore ya jagoranta.
Tau a yau, na tsayu a gaban ku ne, a madadin mahaifan Ahamd da Yan uwa na kusa da na nesa domin mu Mika kokon baran mu ta hannun ku zuwa ga hukumomin da abun ya shafa, domin Neman ayi adalchi akan wannan shari’ar.
Bayan da akayi zaman Kotu wanda kotun Chif Majistare tace ba ta-da hurumin sauraren karar ya kuma mun bukaci Gomnatin Jihar Zamfara ta hannun Ma’aikatar Shari’a shiga cikin lamarin domin zabar kotun da ya dace tayi shara’ar, to tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu, mu mahaifan Ahmad da sauran Al’umma ba mu san inda aka kwana ba, ba muda labarin komai kuma ba mu san inda aka Maida gaba ba.
Wannan yasa zargi a cikin zukatan mu akan tunanin ko akwai wasu Shafaffu da Mai wadanda keda hannu ga lamarin kuma ba a son a bayyana su. Domin a gaban Kwamishinan Yan sanda a lokacin da ya kira ku (Yan Jarida) domin gabatar da mutanen a gaban ku, suka Yi ikirari suka Kuma tabbatar da sun aikata laifin, har shi Aminu Baba ke bada tabbacin cewa shi ke tura yaran su sato mashi ‘ya’yan mutane su yanka su cire kayan cikin su da wasu sassan jikin yaran su sayar mashi, Kuma Ya bayyana kudin da yake biyan su da wuraren da suke haduwa domin ya karba.kudadan. inji Salisu Hafizi “
” Salisu Hafizi ya kara da cewa, shi dai Marigayi Ahmad Yakubu wanda Aka saceshi a ranar 9-12-2021 an tsinci gawar shi a ranar 27-12-2021 wanda bayan kwanaki hudu sai akasamu nasarar chafke wani yaro mai suna Ahmad Tukur dan kimani shekaru goma sha uku (13) inda akasamu bayanai cewar yayansa Abdul yabashi naira dari biyu (N200) yadauki Ahmad Yakub (wato wanda akakashe) zuwa Unguwar Barakallahu inda suka shake shi har ya bar Duniya suka kwashi wasu sassan jikin suka bar shi a cikin wani Kangin Gida, Wanda daga bisani aka tsinci gawar shi (Ahmad Yakub)
Bayan samun wannan bayanin Wanda aka sanar da DSS kuma Allah ya basu nasarar chafke wani Abdul da Abdullahi wadan da sukayi ikirarin wannan aika aikar takisan Ahmad Yakub. inda aka masu tambayoyi suka kuma amsa laifinsu tare da bayyana Aminun Baba wanda yake a anguwa yar hanya kusada tsohon filin jirgi gusau amatsayin wanda suke sayarma sassanin jikin Ahmad Yakub akan.
Yaron (Abdul) yace Aminu Baba ya bashi Naira Dubu Dari Biyar Kasa kuma yanemi ya cikamasa amman yace sai ya dawo kaduna wannan ya faru a ranar 4-01-2022
Bayan da aka samu nasarar kamo Aminun Baba tahannun ‘ya sandan na gundumar gusau ta tsakkiya (Central Division) ya amsa laifinsa tareda bayana wasu mutane wadanda ni Mai magana a gabana yake yi masu bayanin akan wadanda yake yiwa safarar sassan jikin Dan Adam a garin Futua da kuma wani a garin kaduna da kuma wani babban jami’in gwanati da ke Abuja Wanda ba mu San kowaye ba ya zuwa yanzu.
Haka kazalikama, Mai daraja gwamnan jihar Zamfara Alh. Bello Muhammad Matawalle ya halarci ofishin ‘yan sanda na central tare da rakkiyar Kwamishinan Yan sanda CP Ayuba Elkana ya kuma tabbatar da an kamo Aminun Baba da sauraran masu laifin bisaga ikirarinsu, aman abin takaici har yanzu babuwani jaje ko kalaman tausayawa ga iyayen Ahmad Yakubu ko mutanen jaha daga Gwamnan ko gwamnati ko wasu manyan jihar.
A lokacin da ake binciken Aminun Baba munga wani jami’in gwamnatin ya koma bayan Taga ya kira Dan sandan da ke binciken yayi mashi wata magana, tun ya dawo bai sake binciken Aminun ba, Kuma Muna ji lokacin da zai wuce Aminun Baba Yana ce mashi “Mai gida na gode” shi Kuma yace mashi “to sai na dawo” Wanda mu wannan ya daure man Kai.
Bayan kai wadanda ake zargin a kotu a kayi zama na Farko da na Biyu babu wani muhimin lamari da kotu ta aiwatar Wanda muka sani dake nuna alamun wata habbasa wurin nemo hakin jinin Ahmad Yakub. Tun daga lokacin shuru kakeji Babu wata magana takamammiya akan lamarin.
Akan haka ne muke kira ga gwamna Matawallen da kungiyar kare hakin yara da Ministan sharia da su taimaka wajan ganin ayimana adalci akan wannan mumunan zalunci da akai mana. Inji Salisu Hafiz.
