Zaɓen Fidda Gwani A PDP: Dakta Matazu Ya Lashe Zaɓen Sanata a Mazaɓar Katsina Ta Kudu
Daga Hussaini Ibrahim, Funtua
Zaɓen fidda gwani na jamiyyar PDP a mazaɓar Ɗan Majalisar dattawa Katsina ta kudu, Dakta Shehu Abubakar Matazu ya lashe zaɓen Sanata da aka gudanar da shi a shalkwatar mazaɓar da ke cikin Ƙaramar Hukumar Funtua.
Jami’in gudanar da zaɓen fidda gwani, Tanimu Audi ya bayyana haka a lokacin da ya ke bayyana sakamakon zaɓen a Funtua.
Tanimu Audi ya bayyana cewa, mutane biyu ne suka tsaya takara fidda gwanin, wanda suka haɗa, Sani Anani Malumfashi da Dakta Shehu Garba Matazu.
“Jami’in ya bayyana sakamakon zaɓen kamar haka, Sani Anani Malumfashi ya samu kuri’a tamanin da shida (86) sai kuma Dakta Shehu Matazu ya samu kuri’a ɗari biyu da sitin da bakwai (267) dan haka Dakta Matazu ya samu nasara zamowa ɗan takara kujerar Ɗan Majalisar Dattawa na jam’iyyar PDP a mazaɓar Katsina ta kudu. a zaɓen da za’a gudanar shekara ta 2023.inji Tanimu Audi.
A nasa jawabin, Dakta Shehu Matazu ya bayyana godiyar sa ga Allah akan nasara da ya samu da kuma Daliget da suka ga cancantarsa na ya zamo ɗan takarar su. Insha Allah zamuyi iyaka ƙoƙarin na ganin mun ƙara samun karɓuwa ga al’umar yankin Katsina ta kudu dan samun nasara a babban zaɓe mai zuwa.
Mazaɓar Katsina ta kudu ta haɗa da Kananan hukumomin, Funtua, Faskari, Sabuwa, Dandume, Bakori, Danja, Kankara, Malumfashi, Kafur, Musawa da Matazu.
