November 18, 2026

2023: Da Amaechi Ya Zo Katsina, Ya Ce Zai Yaki Talauci Da Rashin Tsaro.

0

Tsohon Ministan Sufuri kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Chibuike Rotimi Amaechi, ya yi alkawarin yaki da rashin tsaro da fatara a kasar nan idan aka ba shi dama ya zama shugaban Najeriya a 2023.

Jaridar LEADERSHIP ta ce, Amaechi ya yi wannan jawabi ne da wakilan jam’iyyar APC a jihar Katsina, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ziyarar tuntubar da ya kai a wannan Litinin din.

Ya ce idan har abubuwa ba su canja ba nan ba da dadewa ba, Najeriya na iya wargajewa ta yadda za a samu rarrabuwar kawuna a tsakanin masu hannu da shuni da talakawa wanda zai kawo illa ga zaman lafiya da tsaro a kasar, inda ya mika kansa a matsayin wanda ya dace don maido da zaman lafiya da tsaro da kuma tabbatar da tsaro a kasar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *