September 18, 2026

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Da Ya Dawo Daga Brazil da Cocaine a filin jirgin sama na Fatakwal.

0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wasu buhunan hodar ibilis guda 24 da aka boye a cikin tayoyi 12 da aka shigo da su cikin kasar nan ta filin jirgin sama na Fatakwal da wani da ya dawo daga kasar Brazil, Okechukwu Francis Amaechi, wanda ya kammala zama gidan kasonshi bayan da aka same shi da laifin safarar miyagun kwayoyi a kasar Amurka ta Kudu.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce mutumem mai shekara 45 da aka yanke ma hukuncin zaman kason, ya fito ne daga karamar hukumar Idemili ta Kudu, a jihar Anambra, inda kuma aka kama shi a filin jirgin saman Fatakwal a ranar Asabar, 7 ga Mayu, 2022 bayan da ya taso daga kasar Brazil.

Kamar yadda jaridar LEADERSHIP ta bayyana, Binciken farko ya nuna Okechukwu, wanda aka kama shi kuma aka yanke masa hukunci a Brazil bisa laifin ta’ammali da miyagun kwayoyi, ya kammala zaman gidan yari a watan Maris din shekarar 2022, bayan da ya yanke shawarar komawa Najeriya da wasu kayan da ya boye fakiti 24 na hodar iblis mai nauyin kilogiram 4.56

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *