November 18, 2026

Allah Ya Baiwa Majigiri Abubuwa 6 Da Ya Cancanta A Zaɓe Shi Gwamnan Jihar Katsina. -Malam Nuraddeen Aliyu Gwanda

0

Malamin addinin Islama a Katsina, limamin Masallacin juma’a wato Sheikh Malam Nuraddeen Aliyu Gwanda, ya bayyana Salisu Yusuf Majigiri na jam’iyyar adawa ta PDP a matsayin wanda ya cancanta a za6a a matsayin gwamnan jihar Katsina a za6ukan shekarar 2023, sakamakon wasu abubuwa guda 6 da Allah ya yi masa tagomashi da su a mahangar addinin Musulunci.

Malamin ya bayyana haka ne a ranar alhamis 31 ga Maris, 2022 a yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron wakilan malamai da suka zo sanya albarka a wajen taro da Wakilan gamayyar magoya bayan jam’iyyar PDP reshen Jihar Katsina suka shirya a garin Mashi, don bikin mika wa Alhaji Salisu Yusuf Majigiri fom din takarar Gwamna da kungiyar ta siya masa.

“Allah ya ci da Majigiri da abubuwa 6 wanda za a iya za6ar shi matsayin Gwamnan jihar katsina a mahanga ta addinin Musulinci.

1.Yana da karfin zuciyar aikata wani abu. Karfi; idan da bai da karfin zuciya to da ba zai iya rike jam’iyyar PDP a jihar katsina matsayin shugabanta ba har shekara 7. Maganganu da yawa sun rika yawo cewa babu irin kalar tuggun da ba a rika kitsawa ba domin a samu hadin kanshi domin ya marawa Gwamnati baya ba, amma ya ‘ki.

  1. Mutum ne shi mai amana. Domin kuwa in da bai da amana, to da ba zai yi adawa ta tsawon shekara 7 ba. Duk babu kalar tayin da gwamnati ba tai mai ba, amma a haka ya rike wannan shugabancin wanda Allah ya dora mashi bisa amana har aka zo in da ake yanzu.
  2. Mutum ne shi mai hakuri. Da yawan al’umma suna shaidar shi a kan cewa shi mutum ne mai hakuri, domin kuwa in da bai da hakuri da kai zuciya nesa, to da yanzu jam’iyyar PDP katsina ba ta zo in da muke a yau ba, balle har wani ko wasu su baro wata jam’iyyar su dawo jam’iyyar PDP don neman wata kujera
  3. Mutum ne shi mai sakankancewa a kan ayoyin Allah. Domin idan ba don Salisu Yusuf majigiri, to da babu wanda zai sha’awar dawowa jam’iyyar PDP a irin wannan 6arnar da gwamatin APC tai wa jihar katsina, domin yanzu a jihar katsina, ba kada wannan zai fadi ma yawan bashin da suka ciyo wa al’ummar jihar katsina a yau , amma yana da yakini cewa idan Allah ya ba shi wannan damar ta zama Gwamna katsina zai yi duk yadda zai yi domin ganin ya ceto al’ummar jihar katsina kan turba mai kyau wanda jihar take a baya tuntuni.
  4. Mutum ne shi mai kiyaye al’amurra, wanda yake kula da amana, wanda yake iya bambanta abinda yake shiga da wanda yake fita, wanda ya san miye Gwamnati
  5. Mutum ne shi masani. Domin kuwa a 6angaren ilimin zamani yayi karatu har zuwa digiri na biyu, ya ma kamata a ce yana koyarwa a jami’a, don haka ta gone 6angare ana iya cewa Salisu Majigiri ya cancanta domin ko ni kaina sheda ne da ni aka yi. Allah ya jikan ran Alhaji Ummuru Musa Yar’aduwa, a lokacin da yake Gwamna babu L.G din da ba mu je ba domin Musuluntar da mutane ana ba su tallafi, ana ba su taimako da wasu Malamai da attajirai. wanda hadda shi Salisu Majigiri din

Haka kuma lokacin da Ibrahim Sheu Shema yana Gwamnan katsina, idan kai lura da yadda Gwamnatin PDP ta taimaki addinin Musulunci, ta gina masallatan juma’a kusan guda 200, ta ci gaba da ba da taimako ga makarantun allo tun da daga tallafin kayan abinci zuwa sutura. dadai sauran abubuwa, wanda gaba ki daya tare da Salisu Majigiri aka rinka aikata wannan abubuwan Alkhairan.

Comrade Mai-Iyali
New Media Aide To
H.E Salisu Yusuf Majigiri
19-05-2022

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *