September 18, 2026

Dakarun Kwastan sun kama kwantena cike da bindigogi a Legas

0

Hukumar hana Fasaƙauri ta Ƙasa (Nigeria Customs Service) ta kama wata kwantena maƙare da bindigogi a Tin Kan Island da ke Jihar Legas a juya Juma’a.

Rahotanni su baiyana cewa mai kwantenan ya yi ƙaryar cewa akwatunan telebijin ɗin bango ne a ciki, amma da ga bisani jami’an Kwastan su ka gano cewa ashe bindigu ne a cikin kwalaye.

Kakakin Kwastan ɗin, Uche Ejesieme ya baiyana cewa jami’an su da ke kan sintiri ne su ka gano kwantenar na ɗauke da bindigu a tama B da ke Tin Can Island.

“Jami’an mu ne su ka tsare kwantenan kuma nan take mu ka rubutawa tama ɗin da kwantenar cikin gaggawa su kuma kai ta ɓangaren bincike domin a san yawan kayan da kuma sauran bayani.

“A halin yanzu dai muna jiran tama ɗin domin a san yawan kayan da kuma masu shi,”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *