September 18, 2026

ASUU: Majalisar Wakilai Ta Saka Baki Bayan Dalibai Sun Rufe Titin Abeokuta.

0

Matamakin kakakin majalissar wakilan Najeriya ya umarci kwamitocin majalissar da abun ya shafa da su saka baki cikin batun yajin akin dake gudana tsakanin gwamnantin tarayya da kungiyar malaman jami’a.

Wase da ya jagoranci zaman majalissar na jiya Larabar, ya dora ma kwamitin kula da harkokin ilimi dana kwadago alhakin sasanta batun, idan kuma suka kasa to majalissar za ta shiga ciki.

Idan dai ba a manta ba, saida shugaban majalissar dattawan Najeriya sanata Ahmad Lawan ya ce majalissarsu za ta saka baki a cikin batun yajin aikin da yaki ci yaki karewa a ranar Talatar da ta gabata, ta hanyar dawo da bangarorin biyu kan tebirin tattaunawa.

Lawan dai ya yi alkawalin ne a lokacin da shugaban kungiyar dalibai ta kasa Dr. Sunday Onuoha ya jagorance su.

Jaridar LEADERSHIP ta ce, dunbun dalibai dai a jihar Ogun sun tarbe hanyar Lagos zuwa Abeokuta don nuna fushinsu akan yajin aikin da kungiyar ASUU ke yi, tare da kwalayensu suna ta rera wakoki akan gwamnati.

Sun rubuta abubuwa akan kwalayen kamar “ A kawo karshen yajin aikin ASUU yanzu” , wasu kuma sun rubuta “Abun Ya Isa Daliban Najeriya Na Shan Wahala Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Saurare Mu”.

Zanga zangar dai ta saka ma ababen hawa cikin wahala.

Da yake magana a madadin daliban, shugaban kungiyar na jihar Kehinde Simeon ya yi gargadin cewa, ci gaba da yin yajin aikin zai kazantar da matsalar tsaron kasar nan.

Ya ce “abun takaici ne ace gwamnatin tarayya na yin siyasa da rayukan daliban Najeriya. Ya ce sun ta maganar a dauki mataki tun kafin fara wannan yajin aikin, amma ASUU da gwamnatin tarayyya suka yi buris.

Shugaban ma’aikata na shugaban kasa farfesa Gambari da ministan kwadago Chris Ngige su ne za su jagoranci zaman tattaunawar tsakanin gwamnati da kungiyar ASUU, dama sauran kungiyoyin da abun ya shafa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *