Zaɓen 2023: Delegates Ɗin Najeriya Na Tsaka Mai wuya Idan Bai yi abinda Ya Da ce Ba
SHAWARA, NASIHA TARE DA JANHANKALI GA MASU ZABEN FIDDA GWANI A JAM’IYYUN SIYASA, WATO (DELEGATE)
Daga shafin Muh’d Auwal Abba Katsina
Daga yanzu zuwa kowane lokaci jam’iyyun siyasa a ƙasar nan za su fara gudanar da zaɓukan fidda gwanayensu, wanda dokar zaɓe ta bada damar a fara tun daga satin farko na April 2022, har zuwa satin farko na june 2022, wanda a karshe za’a miƙawa hukumar zaɓe ta ƙasa cikakkun sunayen ‘yan takara na kowace jam’iyyar siyasa da ke da kudirin shiga zaɓen 2023 zuwa July 2022.
Kamar yadda dokar zaɓen da aka yiwa gyara ta 2021 ta yadda cewa kowace Jam’iyya na da yanci ta zaɓi irin tsarin da takeso cikin tsare tsaren da dokar ta tanada guda uku:
1) zaɓen Kai tsaye, (direct primaries)
2) zaɓen da wakilan da aka zaɓo zasuyi, (indirect primaries), da kuma
3) tsarin yarjejeniya a tsakanin ‘yan takara, (consensus)
Mafi yawan jam’iyyun siyasa a ƙasar nan sunfi karkata akan bin tsarin zaɓe na biyu dana kawo, wato, zaɓen da wakilan da aka zaɓo za su yi (indirect primaries) domin maslahar su, wanda shine musabbabin da naga ya dace inyi wannan rubutu don in tunatar da waɗannan wakilai da zasu gudanar da zaɓuka a kowace jam’iyyar siyasa suke, domin suke da alhakin zaɓo shugannin da zasu jagoranci ƙasar nan a matakin farko.
Da farko yana da kyau delegate ya sani cewa zamanshi delegate nauyi ne babba da ya rataya a wuyansa, wanda tabbas Allah zai tambayeshi akan yadda ya sauke wannan nauyi da aka ɗora masa, shin yayi abun da ya dace? Bai bi san zuciyarsa ba? ko aƙasin haka!
Yana da kyau delegate ya sani cewa idan ya zaɓi san zuciyarsa ya karɓi kuɗi ko yabi umarnin ubangidansa ya zaɓo bara gurbin ɗan takara kowane mataki, to abu biyu ne ke da yiyuwar faruwa:
(i) Jam’iyyarsa zata faɗi zaɓe, a zaɓen game gari, sakamakon zaɓo bara gurbin ɗan takara, saboda yanzu kan al’umma ya fara wayewa daga barin zaɓen duk wanda jam’iyya ta tsaida zuwa ga ɗan takara mai nagarta, wanda asara ne gashi delegate idan Jam’iyyarsa ta faɗi. Ko kuma
(ii) idan ya zaɓi bara gurbin ɗan takara, a karshe ya kasa gudanar da mulki yadda ya kamata, ko ya zalunci al’umma, to a nan idan anje lahira tare zasu tashi a gaban Allah ɗaure da sarƙa, wanda a lokacin kuɗin da ya karɓa ko kuma umarnin maigidansa ba zasu amfaneshi da komai ba.
A ƙarshe yana da kyau delegate ya yi ma kanshi karatun ta nutsu, ya zaɓi abinda yake maslaha a gareshi duniya da lahira, wanda a duniya zaya girbi abinda ya shuka na alheri ko aƙasin haka a lahira ma.
Domin kuwa Allah na cewa: a littafinsa mai tsarki “dukkan wanda ya aikata gwargwadon zarra na alheri zaya ganshi, dukkan wanda ya aikata gwargwadon zarra na sharri zaya ganshi” Allah ya datar damu, amin.
