September 17, 2026

Ni Ɗan Gwagwarmaya Ne Da Na Saba Faɗuwa Zaɓe -QS Mannir Yakubu

0

Daga El-Zaharadeen Umar

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar APC kuma ma’taimakin gwamna Alhaji Mannir Yakubu ya bayyana cewa shi daman can ɗan gwagwarmaya siyasa ne da ya ga jiya kuma ya ga yau.

Alhaji Mannir Yakubu na ɗaya daga cikin ‘yan takara guda bakwai da suka nuna sha’awar su ta tsayawa neman kujerar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar APC a zaɓen 2023.

A Yau juma’a ne ya yi taron manema labarai inda ya ƙara nuni aniyarsa ta neman wannan kujera bayan ya sanar da uwar jam’iyyar sa ta APC acikin wannan satin da ya wuce.

QS Mannir Yakubu ya fada a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai inda aka tambaye shi cewa mulki dai Allah ke bada wa kuma shi ke hanawa, idan har bai damu nasara ba wace matsaya zai ɗauka a siyasance.

Ɗan takarar ya bada amsa da cewa shi mutun da ya saba da gwagwarmaya siyasa saboda haka ya saba ganin faɗuwa tun a shekarar 2003 da 2007 da kuma 2015 inda ya nemi tikitin tsayawa takarar Sanata a Katsina ta tsakiya amma bai samu ba

Daga nan sai ya bada tabbacin cewa idan Allah ya bashi nasara zai ɗora daga inda gwamna Aminu Bello Masari ya tsaya da ayyukan alheri a cikin da bai na jihar Katsina.

Mataimakin gwamnan kuma tsohon kwamshiinan ayyukan gona ya tabbatar da cewa idan Allah ya ba wani ba shi ba, to a shirye yake wajan bada goyon baya ga duk wanda Allah ya ba nasara a zaɓen fidda gwani.

QS Mannir Yakubu ya ƙara da cewa ko lokacin da aka samar da Jami’yyar APC shi ya wakilci jihar Katsina, saboda haka Faɗuwa Zaɓe ba wani bakon abu bane gare shi

kimanin ‘yan takara bakwai da ke akwai a Jami’yyar APC mutum huɗu sun riga sun sayi Fom ɗin takarar su domin shiga zaben fidda gwani da za a gudanar anan gaba.

‘Yan takarar guda bakwai da ake da su sun haɗa da QS Mannir Yakubu da tsohon sakataran gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha Inuwa da Dr. Dikko Umar Raɗɗa da Arch Ahmad Musa Ɗangiwa da Sanata Sadiƙ Yar’adua da kuma AIG Abdulkarim Dauda Daura

Ya zuwa yanzu dai Dikko Umar Raɗɗa da Dr. Mustapha Inuwa da Sadiq Yar’adua da Arch Ahmad Musa Ɗangiwa sun riga sun sayi Fom Ɗin Takarar su ta gwamnan jihar Katsina

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *