Na Amsa Kiran Al’umma Zan Tsaya Masu Takarar Gwamnan jihar Katsina – Hon. Majigiri
Shugaban Jami’yyar adawa ta PDP a jihar Katsina Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana cewa shirye-shiryen sun yi nisa na neman kujerar gwamnan jihar Katsina a zaɓen shekarar 2023 idan Allah ya kaimu.
Honarabul Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana haka lokacin da ya ke tattaunawa da Jaridar Blueink News Hausa ta wayar tarho a jiya Talata.
Alhaji Salisu Majigiri ya kara da cewa sakamakon kiraye-kiraye da ake yi masa na ya fito takarar gwamnan jihar Katsina a karƙashin jamiyyar PDP, na yadda na kuma amince zan fito wannan takarar da zaran na kammala tuntuba kuma saura kiris in kammalata.
A kowane lokaci daga yanza zan iya zuwa baban shalkwatar jami’yyar PDP ta Ƙasa da ke Wadata Plaza, Abuja domin sayo fom ɗin tsayawa takarar insha Allah.
Kasancewar Hon. Salisu Yusuf Majigiri gogaggen ɗan siyasa da ya sha gwagwarmayar tsayawa takarar daban-daban.
Tun daga matakin Kansila da shugaban ƙaramar hukuma da ɗan Majalisar Tarayya da kuma ta Mataimakin gwamna a shekarar 2019.
Haka kuma ya taɓa zama Shugaban Ma’aikatan fadar gidan gwamnatin jihar Katsina lokacin mulkin tsohon gwamnan Ibrahim Shehu Shema
