September 18, 2026

Sayar Da Fom Ɗin Takarar Jami’yyar PDP Na Gwamna Naira Miliyan 21 Koyawa ‘Yan Siyasa Sata Ne -Muttaƙa Darma

0

“Da in zuba kuɗina naira miliyan 21 in sayi Fom na tsayawa takarar Gwamna gara in zuba su a cibiyar horas da sana’o,i da nake da ita a Katsina.”

A wata ganawa da ya yi da masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar Dandume, mai neman takarar kujerar Gwamnan jihar Katsina Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya koka akan yanda aka tsawwala kuɗin fom na tsayawa takarar Gwamnan jiha.

Inda yace “a jam’iyya adawa ace ana biyan kuɗin sayen Fom a kan kuɗi Naira Milyan Ashirin har da ɗaya wannan kamar an buɗe lasisin sata ne ga Gwamnoni,” a cewar shi idan aka haɗa waɗannan kudaɗen ga abinda yake ƙa’ida Al’bashin Gwamna ne na wata goma.

Darma ya ƙara da cewa a shekarar Dubu Biyu da sha Tara Naira Milyan Shidda aka saida Fom, amma yanzu sun maida shi, Milyan Ashirin har da Ɗaya. “Munyi magana da wasu gingima gingiman Ƴan PDP a Abuj inda suma suka yimana ƙorafi akan tsadar Fom ɗin”.

A ƙarshe Injiniya Muttaqa Rabe yace shidai kam bazai sayi Fom ɗin takarar Gwamna ba, akai kasuwa. A wani Faifan Bidiyo na ganawa da Al’ummar ta Dandume Injiniya yace masoya sun ce zasu saimashi Fom, saboda idan Allah ya bada Nasara Al’umma zasu amfanu da waɗannan Ƙudurorin na injiniya, da kum samar wa matasa Aikin yi da koya masu sana’o,i fiye da yanda Cibiyar tasa take yi a yanzu, Inda shi kuma Injiniya yace zai ci gaba da neman mutane.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *