September 17, 2026

TARIHIN WASU DAGA CIKIN DIREBOBIN KATSINA NATIVE AUTHORITY ( NA) DA KUMA DIREBOBIN SARKIN KATSINA, TUN DAGA SHEKARAR 1913 HAR ZUWA YANZU.

0
  1. Alhaji Ulu Kofar Soro.
    Shi Alhaji Ulu sanne ne anan Jihar Arewa. Domin shine farkon Direban da aka fara yi anan Nigeria ta Arewa, domin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944) shine mutum na farko daya fara sayen mota anan Nigeria ta Arewa tun 1913. Alhaji ya fara tuki a shekarar 1913 yayi ritaya a shekarar 1944.
    Shine Direban Sarki Dikko na farko, tun Tarihi ya nuna shine Direban mota na farko a Nigeria ta Arewa baki daya.
    Motar da Alhaji Ulu ya fara tukawa itace Sadly. A wancan lokacin idinbichi goge motar Sarki, Wadanda sukayi aiki tare da Alhaji Ulu sune
  2. Alhaji Da’u Mahi
  3. Mai Arziki
  4. Alhaji Atti Gyare
    Da sauran su.
    Bayan rasuwar Sarki Dikko a shekarar 1944, Alhaji Ulu ya tuka Sarki Usman na watanni ukku, sannan yayi ritaya daga tuki cikin shekarar 1944.
    Daga nan sai aka Koma N. A don dauko wasu daga cikin direbobi. A wancan lokacin DIREBOBIN N. A sune
  5. Alhaji Atti Gyare
  6. Attin Bebe
  7. Alhaji na Hamza
  8. Mijin Yawa
  9. Na Umma Magajin Danko
  10. Alhaji Labaran Zaria.
    Daga cikin Sarki Usman ya nada Labaran Zaria a matsayin Wakilin Mota daga shekarar 1944-1945. Labaran Zaria shine mijin Hajiya Ammacici Yaradua.
    Bayan Labaran Zaria sai aka nada Alhaji Ibro Dan Sarkin Makera Wakilin Mota, Mai kula da gyara motar Sarki.
    Alhaji Saiidu Yaradua, mahaifi ga sendtor Sadiq Yaradua shine Direban Sarki Usman.
    Sai Alhaji Musa Gadi Kofar Soro. Amma Alhaji Said shine babba idan kaga Musa Gadi cikin Mota sai wata Lalura.
    Bayan Alhaji Saiidu yabar Tuki sakamakon wata Matsala, sai Alhaji Musa ya karba.
    Alhaji Sarkin Mota, shine mutum na farko daya fara Sarautar Sarkin Mota a Katsina. Ya fara tuka Sarki Usman a shekarar 1962 ya Zama Sarkin Mota a shekarar 1987. Shi Alhaji Musa Sarkin Mota Yana daya daga cikin mutanen da Sarki Usman Nagogo ya aminta dasu tun ma kamin Nagogo ya Zama Sarki.
    Alhaji Musa Sarkin Mota ya sheda Mani cewa a lokacin da aka ba Sarki Usman Sarauta, Yana zaune a Unguwar Galadunci, gidan da Janar Hassan ya zauna a matsayin Magajin Gari, to a lokacin duk cikin yaran Nagogo Alhaji Musa Sarkin shi kadai Nagogo ta taho dashi gidan Sarki.
    Bayan Alhaji Musa Sarkin Mota ya Zama Sarkin Mota, ya nemi Sarki daya amince mashi da wasu Sarautun mota kamar haka. Wadanda aka amince dasu sune
  11. Alhaji Yunusa Dambo Wazirin Mota
  12. Alhaji Sani Direban Wazirin Katsina a matsayin Kauran Mota
  13. Alhaji Sani second Galadiman Mota da sauransu.
    A halin yanzu Alhaji Yususa Dambo shine Sarkin Motar Sarkin Katsina na yanzu, Kuma Mai Martaba Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman ya nada shi.
    Alhaji Musa Gambo Kofar Soro.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *