November 18, 2026

Wata Tawagar Gwamnatin Tarayya Mai Tantance Yin Bahaya a Fili Ta Kawo Ziyarar Aiki Katsina

0

Tawagar karkashin jagorancin wakilan jihar Katsina, ta ziyarci al’ummomin Danja, da Tsintaiya, da kuma Mandiya.

Shugaban tawagar Mr. Thomson Ema ya bayyana jin dadi bisa abinda suka gani, tare da bukatar al’ummomin yankin su ci gaba da kasancewa cikin irin tsaftar da aka iske su.

Ya bayyana gamsuwa bisa yadda karamar hukumar ta Danja ke gudanar da shirye shirye na masamman masu ilimantar da mutane illar yin ba-haya a fili.

Shugaban tawagar ya bayyana bukatar ganin makarantun Islamiyya, da gidaje, dama sauran inda mutane ke taro suna gina ban-daki.

Wakilin karamar hukumar wanda kuma shi ne daraktan sashen samar da ruwa da tsaftar mahalli ya ce karamar hukumar tsaye take wurin magance yin ba-haya a fili a yankin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *