November 18, 2026

Yadda Talban Musawa, Abdullahi Aliyu (Janar) Ya Zama Hantsi Leƙa Gidan Kowa A Musawa Da Matazu

0

A yanzu maganar da ake yi babu wani matashi da tauraronsa ke haskawa kamar Abdullahi Aliyu (General) wanda ya ke dauke da rawanin Talban Musawa wajan taimakon masu karamin karfi da inganta rayuwar matasan kananan hukumomin Musawa da Matazu a jihar Katsina.

Malam Abdullahi Aliyu (General) Talban Musawa za’a iya cewa kyauta da taimakon da ya sa gaba, abu ne da ya gada tun wajen iyaye da kakanninsa.

Saboda haka duk wanda ya kwana ya tashi a karamar hukumar Musawa ya san yadda iyalansa ke taimakawa ta fuskuki daban-daban da suka hada da bangaran ilimin addinin Musulunci da rawar da mahaifansa suka taka a wannan bigere.

Mahaifinsa wanda jagoran al’umma ne, wanda kullum burinsa ya za’a yi ya taimaki masu karamin karfi da kuma ba da kwarin gwiwa ga matasan sun nemi ilimin addinin Musulunci da kuma na boko kuma ya kafa wani asusu na musamman domin tallafawa ‘ya ‘ƴan masu karamin karfi tun a wancan lokaci ya lura Ilimi shi ne kashin bayan ci gaban kowacce al’umma, wanda dansa Abdullahi ‘General’ ya gada, domin Hausawa na cewa gado girman ɗa.

Yanzu haka Abdullahi Aliyu ya shiga jerin masu rike da sarauta saboda haka shima ya zama basarake, muna iya cewa babu lungu da sakon da aikensa bai kai ba, musamman kananan hukumomin Musawa da Matazu kai ka ce wani hamshakin dan majalisa ne.

Ayyukan da yafi aida hankali akan su ne na gina al’umma da sua hada gina azuzuwa a makarantun islamiyya a lunguna da sakon Waɗannan Kananan Hukumomi na Musawa da Matazu da gina azuzuwa a makarantun boko da biyawa ɗalibai masu karatun makarantun gaba da sikandire ‘yan asalin yankin kudin makaranta.

Hazikin matashin ya yi shura wajan barin kofarsa a bude domin ba kowa dama ta hanhar bada tasa gudunmawar wajen ganin ya Inganta rayuwar matasa da masu karamin karfi a kodayaushe.

Misalin gudunmawarsa a bangaran ilimi shi ne yadda al’ummar jikamshi suka amfana da samun azuzuwa guda biyu a makarantar sikandire ta garin Jiƙamshi tare da gina ofishin zaman malamai domin a samu yanayi na koyo da koyarwa da ya da ce da ilimi.

Haka kuma dan kishin kasar, bai tsaya a nan ba, ya cigaba da wannan aikin na alheri a fannin bunkasa ilimi inda ya ginawa makarantar sikandire ta garin Kurkujan ta gamu da taimakonsa, inda ya gina mata azuzuwa guda biyu da samar da kayan aiki da gina ofis din malamai don ganin dai ta fara gudanar da koyo da koyarwa.

Duk dai da koƙarinsa na koyi da mai girma gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, matashin dan siyasar da kuma taimakawa Ilimin addini Musulunci a waɗannan kananan hukumomin Musawa da Matazu, Talban Musawa ya gina azuzuwan Islamiyya guda biyu a garin Dissi da ke cikin karamar hukumar Matazu.

Bai tsaya haka ba, a bangaren kiwon lafiya, nan ma ‘General’ ya taka muhimmiyar rawa wajen farfado da wasu cibiyoyin kiwon Lafiya, sannan ya gyara dakin haihuwa da na kwantar da masu juna biyu da gyara dakin gwaje-gwaje da sayen gadajen kwanciyar da samar da na’urar gwaji masu lalurar sikila da kuma samar da na’urar bada wutar lantarki watau Janareta a karamar hukumar Matazu.

Abdullahi Aliyu ‘General’ (Talban Musawa) a bangaren noma wanda kusan shi ne al’ummar kananan hukumomin Musawa da Matazu suka fi maida hankali, nan ma ya kai masu gagarumin dauki ta hanyar raba masu takin zamani buhu sama da 600 kuma fa kyauta a daminar da ta gabata.

Manoma sun ji dadin wannan kyautar buhunnan taki kuma ya sha ruwan addu’o’in fatan alheri da ganin shekarar 2023 ya zama dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Musawa da Matazu a zauren Majalisar tarayyar Najeriya.

Idan aka koma bangarana samar da tsaftaccen ruwan sha, Talban Musawa ya gina sabbin rijiyoyin burtsatse masu sarrafa kansu da dama, ya gina makewayin zamani guda shidda a makarantar gwamnati Ta jeKa ka dawo ta ‘yan Mata da ke Musawa.

Sannan kuma wata al’ada da yake da ita duk azumi yana bayar da kyautar buhunnan shinkafa da gero da suga da masara sama da buhunnan dari takwas (800) ga masu karamin karfi da marayu a kananan hukomomin Musawa da Matazu duk shekara.

Talban Musawa kuma dan majalisar tarayya mai jiran gado ya gina wata katafariyar cibiyar bada shawarwari da gyaran dabi’a, ga masu lalurar shaye-shayen miyagun kwayoyi, wadda matar gwamnan jihar Katsina, Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari ta kaddamar a kwanakin baya.

Shin wanene Abdullahi Aliyu (General) kuma Talban Musawa?

An dai haifi hazikin matashin a shekarar 1975 a karamar hukumar Musawa da ke jihar Katsina. Ya fara karatun firamare A Yero firamare da ke Musawa tsakanin shekarar 1980-1986 daga bisani ya wuce zuwa makarantar sakandiren gwamnati da ke Musawa wanda aka sauya zuwa sakandiren gwamnati ta kere-ƙere da ke garin Funtua, Inda nan ya kammala karatunsa na sakandire.

Ya yi karatun share fagen shiga Jami’a a kwalejin horas da Malamai ta Isa Kaita da ke Dutsinma a a alif 1996-1997 daga nan ya samu nasarar samun gurbin karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano, Inda Ya karanci kimiyyar siyasa (Political Science).

Yanzu haka shine mai taikamakawa na musammana Shugaban Hukumar Bunƙasa Kanana Da Matsakaitan Sana’o’i Ta Najeriya (SMEDAN) Dr. Dikko Umar Radda (P.A) kuma ana fatan zai amsa kiran da jama’ar kananan hukumomin Musawa da Matazu suke yi masa na tsayawa takarar dan majalisar wakilai ta tarayya a shekarara 2023 mai zuwa

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *