Yadda Gobara Ta Kama Gidan Mai A Jihar Katsina
Gidan Mai a garin ‘Yantumaki dake a karamar hukumar Danmusa mai suna Sukamos ya kama da wuta.
Kamar yadda Katsina Post ta samu, gidan man wanda yake kan hanya kusa da asibitin garin na ‘Yantumaki ya kama wuta da wutar ne a ranar Talata.
Shaidun gani da ido sun tabbatar wa Katsina Post cewa wutar ta kama motoci biyu dauke da man fetur da aka ajiye a gidan man.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai jama’ar gari ne ke ta kokarin kashe gobarar musamman saboda rashin jami’an kashe gobara a yankin.
Garin ‘Yantumaki dai na kan hanyar zuwa Funtua ne daga garin Katsina kafin akai garin Kankara.
