An Yi Wa Fursunoni 126 Afuwa A Katsina
Daga Katsina Post
Babban Jojin Katsina ya yi Afuwa ga Fursunoni 126 dake zaune a Gidajen Gyaran Hali
Babban Jojin Jihar Katsina Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar, yayi afuwa ga fursunoni 126 da suke zaune a gidajen gyaran Hali da ke Jihar, tare da tura wasu mutum uku domin gudanar da aikin al’umma a jihar.
Waɗanda aka yi wa afuwar sun hada da tsofaffi da masu bukatar kulawar gaugawa ta rashin lafiyar su gami da wadanda aka tabbatar sun canza halayensu zuwa na kirki a zaman su na Gidajen Gyaran Halin.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da Jami’in Hulda Da Jama’a na hukumar Gyaran Hali ta Jihar Katsina Ibrahim Wada ya fitar ga Manema Labarai yana mai cewa an yi afuwa ne ga Fursunonin domin rage yawan cunkoso a Gidajen a faɗin jihar Katsina
Babban Jojin Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ya bayyana cewar ziyarar da ya Kai a Gidajen Gyaran Halin wadda ta biyo bayan afuwa ga fursunonin, bata da nufin yin katsalandan ga hukuncin da alƙalai zasu zartas akan batutuwa da ke gaban Kotu nansu.
Daga nan sai ya yabawa Ma’aikatan Hukumar Gyaran Halin akan jajircewarsu ga aiki, tare da yin kira akan su dore da yin hakan.
Tunda farko, Babban Jami’in Hukumar a Jihar Katsina Muhammad Abdulmumin Haruna, yace rage cunkoso a gidajen, zai basu sukuni na gudanar da aikinsu yadda ya kamata na daidaita akidar mazuna Gidajen da aka yiwa hukunci, tare da maida su a cikin Al’umma.
Ya ce hakan zai bada dama wurin ganin sun komawa al’ummomin su da halaye na gari kuma a cikin salama
