Ɗan Majalisar tarayya Hon. Sani Aliyu Ɗanlami Ya Ziyarar Taaziya Ga Tsohon Kakakin Majalisa
Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumar Katsina ta tsakiya Hon Sani Aliyu Ɗanlami (Mai Raba Alheri) ya kai ziyarar ta’aziya ga tsohon kakakin majalisar dokoki Hon. Yau Umar Gwajo-gwajo akan rasuwar mahaifinsa.
A lokacin wannan ta’aziya ɗan majalisar ya yi addu’ar neman gafara ga mamacin tare da rokon Allah ya basu hakurin jure wannan baban rashi.
Daga cikin waɗanda suka raka ɗan majalisar akwai tsohon sakataren ilimin na ƙaramar hukumar Katsina Alhaji Mannir Yahaya da shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Katsina da sauran jama’a a cikin tawagar
