November 18, 2026

Ɗan Majalisa Ya Ɗauki nauyin Biyan Kudin Makarantar Ɗalibai 60 a Katsina.

0

Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tsakiya Hon. Sani Aliyu Ɗanlami Mai Raba Alheri ya sake kafa tarihi inda ya ɗauki nauyin biyan kuɗin karatun ɗalibai yan asalin ƙaramar hukumar Katsina su 60.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗaliban za su yi karatu ne a reshen jami’ar Ahmadu Bello wanda take da mazauni a kwalejin ‘ Gial College of Higher Education, Katsina ‘ domin yin karatu a ɓangarori da dama.

Da yake ƙaddamar da bada wannan tallafi ɗan majalisar wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa na musamman Hon. Abdulrazaq Yahaya ya ce wannan wani ɓangare ne na alƙawarin da Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ɗauka a lokacin yakin neman zaɓen sa.

A cewar sa, ɗalibai 60 ne za su amfana da wannan tallafi, kuma an zaɓo su ne daga cikin ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya domin su amfana da wakilcin ɗan majalisa.

‘Wadannan Ɗalibai za su karatun difolama ne a kwalejin ‘Gial College of Higher Education ‘ a ɓangarori guda shida da suka haɗa da bangaren turanci da ilimin lissafi da ilimin kimiyyar ɗakin karatu da kuma ɓangaren Hausa’ inji A.Y

A cewar sa, sauran kwasa-kwasan sun haɗa da da bangaren Addinin Musulunci da kuma ilimin kimiyya da zumar cewa sune kashi na farko kuma ana sa ran cewa nan gaba kaɗan wasu ma za su amfana a sauran ɓangarori

Hon. Abdulrazaq Yahaya ya ja kunnen ɗaliban da su maida hankali a wajen wannan karatu na su domin su zama madubi ga sauran al’umma tare da fita kunyar wanda ya ɗauki nauyin karatun na su.

Daga karshe ya yi masu fatan alheri tare da karfafa masu gwiwa na su yi karatu shi ne kaɗai hanya mafi sauki na cin moriyar wannan duniya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *