Za a Ga Canji A Harkar Tsaron Najeriya Nan Bada Jimawa Ba – AIG Sadiƙ Abubakar
Daga Babangida Sunusi, Kano
An bayanna yunkurin hukumar ‘yan sandan Najeriya ƙarƙashin jagoranci Usman Baba Alkali wajen ganin an samar da ƙarin cigaba da tsaro da kayan aiki a ƙasar nan.
Bayanin hakan ya fito daga bakin mataimakin shugaban ‘yan sandan mai wakiltar shiyyar Kano da Jigawa watau AIG Sadiq Abubakar Baba yayin taron ƙaddamar da manyan motoci guda biyu da shugaban Kamfani Triple K, Alhaji Najib Jafar Koguna ya bama Mopol lamba ta tara da ke ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano.
AIG Sadiq Abubakar Baba ya kuma ƙara da cewa a ƙoƙarin shugaban ‘yan sanda na ƙasa wajen ƙara kawo canji wajen tabbatar da zaman lafiya da kare hakkin al’umma.
Haka zalika ya kuma ƙara da cewa yana da yakinin shugaban ‘yan sanda na ƙasa na aiki kan yadda zai ƙara samama jami’an ‘yan sanda gurin zama mai kyau da kayan aiki dan cigaba da bada himma wajen kare hakkin jama’ar ƙasar nan da rayukansu.
Sannan ya kuma bukaci sauran masu hannu da shuni na jihar Kano da Jigawa da su Kara shigowa dan ƙara taimakon jami’an tsaro da damar da Allah ya basu dan ganin an samu cigaba da zaman lafiya.
Kuma ya ja hankalin jami’an da ke kula da yanki na tara wajen ganin sunyi amfani da wannan motoci ta hanyar da ya dace tare da kula dasu yadda yakamata, sannan sukama samama masu direbobi nagari dan samu damar amfani da su a tsawon lokaci.
Shima Alhaji Najib Jafar Koguna yace lallai matsayin da Allah ya basu da damar da suke da ita ya ƙara jan hankali wajen sama masu motoci dan gudanar da aiki cikin sauki.
Alhaji Najib ya kuma ce taimakon jami’an tsaro kamar ya taimaki al’ummar shine, dan kuwa aikin jama’a ne da ƙasar nan dan haka ba wani abin wahala bane kowa yana da kyau ya taimaki jami’an tsaro musamman ‘yan sanda suna matuƙar ƙoƙari wajen kare al’umma da dukiyoyinsu.
Daga karshe yace nan bada jimawaba zasu ƙara gabatarma da zone na ɗaya da shalkwatar suma nasu motocin guda byu-biyu dan cigaba da gudanar da aikinsu na kare jama’a da dukiyarsu.
