September 18, 2026

Yadda Wata Matashiya ta Kuɓuta Daga Cin Zarafi A Wajen Shugaban Ma’aikatar Da Take Aiki A Katsina 

PhotoCollageMaker_20241220_175826055

Daga Maryam Mukhtar, Katsina 

Mata, jinsi ne mai matukar muhimmanci da baya misaltuwa a cikin kowace irin al’umma, domin su ne jigon samun kowace irin nasara da cigaban al’umma, kamar yadda Hannatu Mohammed, Shugabar kungiyar mata ‘yan jarida reshen jihar ta sanar a yayin zantawa da ita.

Ta kara da cewa idan jinsin mata suka samu kulawar da ta dace to tabbas za a samu nagartaciyar al’umma da za ta yi fice a duk fannoni na rayuwa, kama daga tattalin arziki, ilimi da zamantakewar rayuwa. Idan kuma aka samu akasin haka, to sakamakon ba zai zama kyakyawa ba.

Cin zarafin jinsi shi ne tauye ‘yancin mata ko maza ta hanyar musguna masu ko ɗora masu abin da ya fi karfinsu da kuma keta alfarmar da mahalicinsu ya yi masu, kamar yadda Kamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano ya rawaito.

A cikin rahoton shekarar 2006 da aka buga a shafin yanar gizon Asusun Ƙarfafa Mata na Majalisar Dinkin Duniya (UNIFEM), Kofi Anan, Tsohon Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya bayyana cewar: Cin zarafin mata da ‘ƴan mata matsala ce da za a iya daidaita ta da adadin annoba.

A kan samu Aƙalla ɗaya daga cikin mata uku a duniya da ake yi musu bugun tsiya, a tilasta musu yin jima’i, ko kuma akan ci zarafinsu a fannoni daban-daban.

Akwai hanyoyi daban-daban na cin zarafin jinsi wanda wasu ana yin su da sunan al’ada wanda kuma yana bambanta a tsakanin al’umma misali, Auren dole, Hana yara zuwa makaranta, Dora ma yara tallace-tallace a titina kasuwa da kuma Tasha, Tura yara mata aikatau, Horo mai tsanani, Bambantawa tsakanin mata da maza da kuma jahilci wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen cin zarafi musamman ga jinsin mata, a cewar Farfesa Bahir Aliyu Sallau na sashen nazarin harshen Hausa a Jami’ar Tarayya FUDMA, da ke Dutsinma, jihar Katsina.

Ya kara da cewa matsalar Cin Zarafin Mata; na da dogon tarihi, domin kuwa ya daɗe yana faruwa.

Hajiya Hannatu Mohammed

Hindatu daya daga cikin waɗanda suka tsira daga cin zarafi daga hannun shugaban ma’aikatar da take yi wa aiki, ta bayyana irin damuwa da halin kuncin da ta samu kanta a lokacin da lamarin ya kusa faruwa da ita.

Lamarin kamar yadda ta ce “da farko soyayya muka fara, kasancewar bani da aure. Ni kuma na fara sonsa tsakani da Allah, amma a hankali, sai ya fara bijiro min da wasu alamomi da maganganun da ban fahimci abin da yake nufi ba.

“Ana haka, kwatsam wata rana ya nuna wata alama da ke nuna lallai ga abin da yake nufi, na fara ja baya da harkokinsa. Kasancewar ina ƙarƙashin ikonsa a inda nake aiki, sai ya fara nuna min tsana da kyara, saboda waccan damar da na hana shi.

Shugaban ma’aikatar da nake aiki ya kafa min kahon-zuƙa inda yake ta bullo min da dibaru daban-daban na neman cin zarafina. Wannan yunkuri nasa, ya sa har na rasa aikina a ma’aikatar.

Sanarwar Majalisar Ɗinkin Duniya a kan ƙoƙarin kawar da cin zarafin mata ta bayyana cewa: “cin zarafin mata wata alama ce ta rashin dai-daito tsakanin maza da mata a tarihi”.

Jihar Katsina, jiha ce da ke a Arewa maso Yammacin Nijeriya wanda mafiya rinjayen al’ummar da ke rayuwa a jihar suka kasance Hausa Fulani kuma cin zarafin jinsi na faruwa a jihar nan da can a fannoni mabambanta.

Cin zarafi matsala ce da ke ci wa al’ummar yankin tuwo a kwarya wanda hakan ya sa gwamnati, kungiyoyi, malaman addini, sarakunan gargajiya da kuma masu ruwa da tsaki suka tashi tsaye domin ganin sun yaki wannan dabi’ar don ganin an shawo kan matsalar musamman kasancewar jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ke fama da kaluballen tsaro kuma ɗaya daga cikin jihohin da ke da yawan rahoton cin zarafi musamman ga mata da yara ta yadda za a samu cigaba mai dorewa da cigaban tattalin arziki al’mmar jihar.

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa

Daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina ke yi na dakile cin zarafin ya hada da sa ma dokar hana cin zarafin jinsi hannu da gwanan jihar Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi a watan Disambar shekarar 2023 (VAPP) domin gurfanarwa tare da hukunta masu aikata laifin da kuma kare hakkin mata da yara.

Sai kuma kirkirar kotun tafi da gidan ka domin kula da cin zarafin jinsi, tare da kirkirar cibiyar da za ta rika kula da wadanda aka ci zarafinsu.

Aikin cibiyar shi ne kai rahoton cin zarafin ga hukumar ‘yan sanda domin yin bincike, kulawa da lafiyar su da kuma samar da hujjar cewa an ci zarafinsu da kuma wayar da kan waɗanda suka tsira daga cin zarafin tare da nuna musu ba wannan bane ƙarshen rayuwa ba tare da koya masu sana’oi gami da ba su tallafi domin dogaro da kai.

Mai Dakin Gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulahat Dikko Raɗɗa

A ranar 15 ga watan Disambar, 2024 ne Mai ɗakin gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Radda ta bayyana cewa gwamnati ba za ta zuba ido ba a rinka yin barna ba, za su jajirce wajen kawo karshen cin zarafin jinsi, inda ta ƙara da cewa rayuwar aure rayuwar soyyaya ce da darattawa babu inda aka ce namiji ya wulakanta matarshi ko ‘ya’yanshi ba a bashi damar cin zarafin su ba.

Ta bayyana irin hukuncin da za a ɗauka ga waɗanda aka kama su da laifin cin zarafi da cewa za a buga su a jarida, gidajen Talabijin da Radiyo domin duniya ta gansu.

Hajiya Rabi Muhammad babbar jami’a da ke kula da ɓangaren cin zarafin jinsi ƙarƙashin ma’aikatar mata ta jihar Katsina ta ce daga cikin ƙoƙarin gwamnati na dakile cin zarafin jinsi ya haɗa da kirkirar sashen da ke kula da cin zarafin jinsi, fahimtar da al’umma hakkin junansu da kuma kare hakkin juna, kula da waɗanda aka ci zarafin su da ba su shawarwari da ɗora su akan hanyoyi managarta da kuma tsaya ma wanda aka ci zarafin su har zuwa matakin shari’a

Hajiya Hannatu Muhammad na daga cikin mata masu kare hakkin mata da yara kuma shugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta jihar Katsina ta ce wajibi ne kulawa da mata da yara tare da kare hakkokin su da martabar su domin duk wani cigaba da za a samu akwai gudumawar da mata suka bayar inda ta ba da misalai akan cin zarafin jinsi da irin ƙoƙarin da kungiyar ke yi na kwatar ma mata da yara ‘yancin su da aka take a makarantu, ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu, gidajen aure da sauransu.

Ta kuma yabawa gwamnan jihar Katsina bisa yadda ya ke gaggawar ɗaukar mataki akan abin da ya shafi mata da yara misali yi ma makarantar koyar da sana’oi garambawul tare da sake wasu daga cikin mahukuntan makarantar, ta kuma taɓa korar wani shugaban makarantar sakandire da aka kama da laifin yi ma ɗalibarsa ciki.

Kwamandan Hisba Abu Ammar

Bisa ga ƙoƙarin malamai kuma akan dakile cin zarafin jinsi sun ce babu inda shari’ar musulunci ta amince da cin zarafin mata. Dr. Muhammad Aminu Usman ( Abu Ammar) malamin addini ne kuma shi ne Baban Kwamandan Rundunar Hizba ta jihar Katsina ya kawo misalai da ayoyi da hadisai akan yadda addinin Musulunci ya ba da fifiko akan mata da kuma yadda kula da su ya zama wajibi.

Ya kuma bayyana irin dalilan da suke sanya wa ake samun cin zarafin jinsi da suka haɗa da rashin ilimin zamantakewar rayuwa, talauci, Rashin bincike yayin aurar da ‘ya’ya mata, hana hukunta mai laifin daga iyayen waɗanda aka ci zarafin yayansu, rauni ga kotuna da kuma amsar cin hanci daga masu laifi.

Kazalika, ya bayyana matakan shawo kan matsalar da wayar da kan al’umma game da hakokin junansu musamman a zamantakewar aure, Tallafa ma marasa karfi a cikinsu musamman mata, hana dora ma yara tallace-tallace da kuma tsaurara hukunci ga wanda aka kama da laifi.

Tabbas sanya iyayen ƙasa acikin wannan hidimar na taka muhimmiyar rawa kasancewar sune iyayen al’umma kuma makusanta ga al umma suna zama ido ga mahukuntan wajen miƙa masu laifi ga hukuma ko da kuwa waɗanda aka zalunta sun ki kai koke.

A ɓangaren iyayen ƙasa kuwa watau sarakunan gargajiya Danmadamin Kafur, Alhaji Abdulmutalib Rabe Kafur yace idan ana son samun nasarar yaki da cin zarafin jinsi to sai an dawo ma da iyayen ƙasa ta yadda za su iya yin hukunci tare da dawowa kan turbar adinin musulunci da kuma al’adar mu ta Hausa Fulani da muka bari, yin bincike kafin a aurar da yarinya da kuma tursasa ma iyaye maza ɗaukar nauyi ilimantar da ‘ya’yansu, ba su tarbiya kulawa da cinsu da lafiyar su tare da hukunta duk wanda aka kama da laifin cin zarafi ba tare da yin la’akari da kuɗin shi, mukami ko kuma matsayinshi a al’umma ba.

About The Author