September 19, 2026

Sanata Yakubu Lado Mutum Ne Mai Runtan Aiki Cewar Dilkko Raɗɗa

0

Ɗan takarar kujerar Gwamna jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar APC Dakta Dikko Umar Raɗɗa ya maidawa Sanata Yakubu Lado martani da cewa shi mutun ne mai runtan aiki.

Dikko Raɗɗa ya ce hanyar Raɗɗa da Lado ke cewa ta lalace kuma duk wanda zai bita sai ya nemi takalmi shi ya yi ta lokacin yana shugaban ƙaramar hukumar Charanci.

Ya ƙalubalanci Sanata Lado da ya nuna hanyar da ya yi lokacin yana shugaban ƙaramar hukumar Ƙanƙara, hatta hanyoyin da yaki ikirarin anyi a ɗanmarke da ƙanƙara, gwamnatin APC ce a ƙarƙashin shugaba Muhammad Buhari aka yi ta a shekarar 2018

Ɗan takarar ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da kafar sadarwa ta DCL Hausa inda ya ƙara da cewa hukumar da ya yi aiki bata da hakkin yin kowace irin hanya, abinda kawai suke yi shi bunƙasa ƙananan da matsaƙaitan sana’o’i.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *