September 17, 2026

NSCDC Ta Bankaɗo Masana’antar Ƙera Makamai Kirar Gida A Katsina 

IMG-20260228-WA0007

 

Rundunar tsaron farin kaya ta NSCDC ta yi nasarar gano wata masana’antar ƙera makaman gida a garin Korea da ke karamar hukumar Ɓatagarawa a jihar Katsina

 

Wannan samame ya faru ne a ƙarƙashin jagorancin kwamadndan rundunar na jihar Abbas Ɗan-ile Moriki a kokarin da na inganta harkar tsaro a jihar Katsina

Bayanin haka na kumshe ne a cikin sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SC Buhari Hamisu ya fitar aka rabawa manema labarai a Katsina

 

A cewar sanarwar, ranar Alhamis 26/02/2026 da misalin karfe 10:00 na safe rundunar ta samu wasu rahotanni sirri inda ta kai da rushe wannan haramtacciyar masana’antar ƙera makaman gida a kauyen Kore da ke kan hanyar Batsari

Kazalika rundunar ta yi nasarar kama mutane huɗu da ake zargi da ƙera makaman gida a wannan masanaantar da suka haɗa da Haruna Lawal da Badamasi Kabiru da Hamza Lawal da kuma Sagir Abba

 

Haka kuma an samu bindigogi kirar gida guda takwas da wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen wannan danyen aiki tare da mashina guda biyu kirar jincheng a lokacin samamayen

Sanarwar ta cigaba da bayanin cewa yanzu haka ana gudanar da bincike domin gano sauran abokan hulɗar da kuma masu sayen makaman.

 

A halin yanzu ana ci gaba da bincike domin gano sauran ‘yan ƙungiyar da masu sayen makaman. Rundunar ta tabbatar da cewa za a bi dukkan matakan doka wajen gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

 

Daga ƙarshe rundunar tsaro ta NSCDC ta jadadda kudirin ta na cewa ba zata yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da yawaitar makamai ba bisa ka’ida ba tare da toshe duk wata hanya ta ayyukan miyagu

 

Sannan kwamandan Rundunar NSCDC Abbas Ɗan-ile Moriki ya godewa al’umma akan irin haɗin kai da suke baiwa rundunar su domin samun nasarar da ake bukata wajen yaƙi da ta’adanci a jihar Katsina da ƙasa baƙi da

About The Author