Ku Fito Ku Yi Katin Zaɓe Domin Zaɓar Nagartattun Ƴan Takarar Da APC Ta Tsaida A Matakai Daban-daban. -Shugaban Jam’iyyar APC, Alhaji Sani Daura
Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Aliyu JB ya yi kira ga al’umma da su fito su yanki katin Zaɓe da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Kasa ke cigaba da yi a halin yanzu domin fitowa ranar babban zaben da ke karatowa a shekarar 2023 domin zaɓar nagartattun yan takarar da Jam’iyyar APC ta tsaida a kujeru daban-daban dake fadin kasar nan domin cigaba da sharbar romon damakaradiyya.
Alhaji Sani Aliyu JB ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da manema labarai kan jaddada muhimmancin yin katin zabe a Katsina.
Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Da Aliyu Daura ya cigaba da cewa yin katin zabe yana da matukar muhimmanci da bai misaltuwa, saboda dole sai da shi ne ranar zabe za ka iya yin zabe, ka zabi wanda ka ke so domin ganin an samu cigaba mai dorewa.
Yana da kyau ga duk wanda ya kai shekarun yin zabe, musamman wanda ba ya da shi ko kuma wanda na shi ya bata da ya hanzarta zuwa ofishin Hukumar zaɓe mai Zaman Kanta Ta Kasa mafi kusa da shi don ganin ya yi rijistar kafin wa’adin rufewa.
Daga karshe, shugaban Jam’iyyar APC a jihar Katsina, Alhaji Sani Aliyu ya yi kira da babbar murya ga duk wanda bai samu damar yi ba, saboda yadda yan uwanmu na kudanci Najeriya suka maida hankali wajen ganin sun mallaki katin zabe, don haka mu ma anan ya kamata mu kara jawo hankalin al’umma da su yi rijistar katin zabe.
