Katsina Ta yi Cikar Farin Ɗango da Mahalarta Daurin Auren ‘Ya’yan Sanata Yakubu Lado
Garin Katsina ya cika makil da manyan baki daga sassa daban daban na kasar nan da suka halarci daurin auren ‘ya’yan jigon dan siyasa kuma hamshakin dan kasuwa, Senata Yakubu Lado Danmarke, a masallacin Juma’a na Bani Commassie da ke Katsina.
‘Ya’yan nasa mata da aka aurar su ne Rukayya da Maryam da Fatima da Dr. Zainab Yakubu Lado wadanda hamshakin dan kasuwa Alhaji Dahiru Bara’u Mangal ya kasance waliyyinsu a madadin Sanata Lado.

Aurarrakin sune na Rukayya Yakubu Lado da angonta Abubakar Zaharaddeen wanda tsohon babban hafsan sojin sama, Air Vice Marshall Sadiq Abubakar, ya karbar masa auren da kuma Fatima Yakubu Lado da angonta Khalid Kabir Barkiya wanda mahaifinsa Sen. Kabir Barkiya ya amsar masa auren.
Hakazalika, an daura auren Dr. Zainab Yakubu Lado da Farfesa Wasiju Madina Almustafa wanda Gwamna Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya amsar masa auren.
Ta hudunsu ita ce Sabira Yakubu Lado da angonta Aminu Abubakar Musa wanda Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi ya zama wakilinsa a amsar auren.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ne ya tarbi manyan bakin Kuma ya raka su zuwa wurin daurin auren tare da sauran manyan baki da suka hada da ‘yan majalisar tarayya da na jiha da hakimai da sauran masu rike da sarautun gargajiya da manyan ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na kasar.
Daurin auren ya kuma samu halartar ‘ya’yan jam’iyyar PDP daga dukkan mazabun jihar Katsina 361, har ma da jiga-jigan jam’iyyar da dama, cikinsu har da tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Mustafa Inuwa.

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) reshen Jihar Katsina, Sheik Yakubu Musa Hassan, shi ya jagoranci addu’o’in samun zaman lafiya ga anguna da amaren, tare da addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban kasa.
Yakubu Lado dai tsohon Sanata ne, tsohon dan majalisar wakilai, tsohon mamba a hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC), tsohon shugaban karamar hukumar Kankara kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Katsina karo uku.

Ya kuma yi fice wajen tallafa wa masu karamin karfi, da mata, da matasa, da dalibai, da ‘yan gudun hijira, da gajiyayyu, da zaurawa, da maratu, da marasa galihu, da ‘yan siyasa a dukkan matakai.
