Jihar Katsina Bata Saidawa Ba Ce: Gargaɗin Ɗalibai Ga Masu Zaɓen Fidda Gwani (Delegates)
A ya yin da ya rage ƙasa da kwana guda a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki jihar Katsina gamayyar kungiyoyin ɗalibai ‘yan asalin jihar Katsina sun gudanar da zanga-zangar lumana inda suke yi kira ga Delegates da su zaɓarwa jama’a mutanen kirki.
Wannan zanga-zangar lumana dai ta samu halartar ɗaruruwan ɗalibai da suka fito domin nuna takaicinsu game yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da kuɗi wajan sayen masu zaɓen fidda gwani (Delegates) domin su zaɓi abinda ya saɓa da ra’ayin mafiyawan jama’a.
Haka kuma wannan zanga-zanga na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan takarar da magoya bayan su da su kansu al’umma ke zargi kamar ba za a yi masu adalci ba a zaɓen fidda gwani da za a yi.
Ita dai wannan zanga-zanga da ta haɗa mata da maza ɗalibai ta fara ne daga kusa da kamfanin saida wayoyi na continentel computer sannan ta ƙare a shatale-telan gidan Rodi da ke Katsina ba tare da wata tarzoma ba, kuma ta samu rakiyar jami’an tsaro.
Ɗalibai dai sun riƙa tafiya suna rera wakoki na jan hankali ga masu zaɓen fidda gwani (Delegates) tare da ɗaga kwalaye ɗauke da rubuce-rubucen sakon da suke son isarwa
Daga cikin rubuce-rubuce akwai wanda aka rubuta Katsina ba ta saidawa ba ce da kuma wanda aka rubuta fiye da mutane miliyan 8 makomarsu a siyasa tana hannu masu zaɓen fidda gwani (Delegates) saboda haka su yi abinda ya da ce.
Da yake jawabin rufe wannan zanga-zangar lumana jagoran tafiyar kwamared Aliyu Mamman Ɗan Umma ya bayyana cewa sun fito wannan zanga-zanga ne domin nuna takaicinsu akan yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da kuɗi wajan zabarwa al’umma ‘yan takarar jeka na yi ka saboda mummunar manufa ta siyasa
“Delegates ku duba halin da jama’a ke ciki ku zaɓi mutanen kirki waɗanda talaka zai amfana da shugabancinsu duba da irin halin da wannan ƙasa da arewacin Najeriya da ma jihar Katsina suka shiga ciki.” Inji shi
Ya ce ya kamata a zaɓi mutamin da zai duba matsalar tsaro da ke damun jihar Katsina da fatara da talauci da suka yi wa jama’a ɗaurin huhun goro, kuma kadda su duba ‘yan kuɗin da za a ba su wanda za su ƙare su bar su da mutane kuma a cigaba da shan wahala tare
Kwamared Aliyu Mamman ɗan Umma ya ƙara da cewa ranar gobe kiyama za a tambayeku (Delegates) abinda kuka aikata dangane da makomar al’ummar jihar Katsina da take da fiye da mutane miliyan takwas.
