Hukumar Kula Da Shige Da Fita Ta Kasa na Neman Ɗaukin Gwamnatin Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) reshen jihar Zamfara ta bukaci daukin gwamnatin jihar Zamfara da ta gyara hanyar da ta kai ofishinta na Saminaka da ke cikin birnin Gusau.
Kwantirolan jihar, Ibrahim S Dauda ne ya yi wannan rokon a lokacin bikin cika shekaru 60 da kafa hukumar shige da fice ta Najeriya.
Acewar sa, Matsalar hanyar lokacin damina bata biyuwa sai da zagaye da ‘yan dubarbaru muke iya shiga Hedikwatar dan gudanar da ayyukan mu.
Don haka muke rokon gwamnatin jihar ta taimaka wa rundunar wajen gyara hanyar domin shiga ofishinsu cikin sauki.suma alummar unguwar gyaran hanyar zai taimaka wajan bankasa rayuwar su.
Da ya koma kan batun bikin cikar hukumar shekaru 60 a Kwantilora ya bayyyana cewa, hukumar ta samu nasarori da dama. ya kuma yi kira ga masu son zuwa Najeriya da su tabbatar sun samu takardun tafiye-tafiyen da suka dace don gudun kada a mayar da su kasashensu.
Ya kuma yabawa gwamnatin jihar Zamfara bisa dukkan goyon bayan da take baiwa hukumar shige da fice ta jihar tare da rokon gwamnatin jihar Zamfara da ta tallafawa kokarinta na wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Ya yi kira ga jami’an rundunar da su rika sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a kodayaushe domin rundunar ba za ta amince da duk wani aiki na rashin da’a ba.
