September 18, 2026

Gwamnatin Tarayya Ta MiƘa Gidaje Ga Masu Amfana da Shirin ‘Rent-to-Own’ a Abuja

IMG-20260625-WA0027

 

Gwamnatin tarayya ta miƙa gidaje ga masu cin gajiyar shirin mallakar gida na ‘Rent-to-Own’ a Bungalow City da ke kan titin Dei-Dei–zuba a Abuja, a wani mataki na ƙara samar da gidaje masu arha ga ‘yan Nijeriya.

 

Ministan gidaje da raya birane, injiniya Muttaƙa Rabe Darma, ne ya jagoranci bikin miƙa makullan gidajen, inda ya jaddada kudirin gwamnatin shugaba Tinubu na tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya ya samu damar mallakar gida.

 

Ministan ya bayyana cewa shirin na daga cikin manufofin gwamnatin tarayya na rage matsin lambar kuɗin haya da ke addabar ma’aikata da sauran mazauna manyan birane. Ya ce gwamnati ta himmatu wajen cika alkawarin samar da matsugunne mai inganci da arha, tare da tabbatar da cewa duk waɗanda suka amfana da shirin za su karɓi makullan gidajensu kafin ƙarshen shekarar nan.

 

A nasa jawabin, manajan darakta kuma babban jami’in gudanarwa na bankin lamunin gidaje na Nijeriya (FMBN), Shehu Usman Osidi, ya ce an fuskanci wasu ƙalubale a farkon aikin bayan an ware wani ɓangare na gidajen ga hukumomin tsaro.

 

Sai dai ya bayyana cewa haɗin gwiwar da aka yi tsakanin bankin lamuni da kamfanin Brains & Hammers Limited, tare da sa hannun Ministan, ya taimaka wajen warware matsalolin da kuma tabbatar da cewa masu rajista sun samu gidajensu.

 

Da yake magana a madadin masu anfani, Barista Sanusi Sa’idu Ɗantsoho ya yaba wa gwamnatin tarayya da bankin lamuni bisa samar da damar mallakar gida ga ‘yan Najeriya. Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da faɗaɗa irin waɗannan shirye-shiryen a faɗin ƙasar domin bai wa ƙarin jama’a damar mallakar gidaje na su arha

About The Author