Gwamna Raɗɗa ya yi ta’aziyyar Rasuwar Sardaunan Sokoto Alhaji Abubakar
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya yi ta’aziyyar rasuwar tsohon ministan kuɗi kuma Sardaunan Sokoto Alhaji Abubakar Alhaji wanda ya rasu a ranar Alhamis a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.
“Yau Nijeriya ta yi rashi ɗaya daga cikin waɗanda suka bauta mata jihar Sakkwato ta rasa jigo abin koyi wanda rayuwarsa ta ƙare wajen kare mutuncin aikin gwamnati da nuna kishin ƙasa” inji Raɗɗa.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana rashin Sardaunan Sokoto a matsayin wani jigo kuma dattijo masanin tattali arziki, ɗan kishin ƙasa wanda ya yi aiki da gaskiya a wurare daban-daban masu mahimmanci a matakin ƙasa.
A cewar gwamna Raɗɗa Abubakar Alhaji Alhaji shugaba ne da za a riƙa tunawa da shi ta hanyar basirar sa da jin ƙansa da jajircewar sa wajen aikin al’umma ta sanya ake girmama shi a Nijeriya a iya tsawon rayuwarsa.
Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa marigayi ya sadaukar da rayuwar sa wajen yi wa ƙasa aiki da cigaban jihar Sakkwato wanda ya bar wani tarihin da za a riƙa tunawa da shi a matsayin shugaba wanda baya san kan sa.
“A daidai lokacin da muke wannan juyayi wannan babban rashi, muna tuna irin sadaukarwar sa ga al’umma da ƙasa wajen ganin ya bar wani abu da za a riƙa tunawa da shi a matsayin shugaba” inji Raɗɗa
Kazalika gwamnan ya miƙa ta’aziyyar da ga gwamnan jihar Sakkwato Ahmad Aliyu Da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar da iyalan marigayi da gwamnati da sauran al’ummar jihar Sakkwato da Nijeriya baƙi ɗaya
Ina rokon Allah ta’ala ya jikan Sardaunan Sokoto da Rahama ya sanya Aljanna ta zama makoma a gare shi, sannan ya baiwa iyalansa da ƙasa baki ɗaya hakurin rashin sa.
