Ana zargin wani Ɗalibi Ya Kashe abokinsa Saboda ɓatan Farantin Abinci a jihar Kwara.
Wani dalibin kwalejin ilimi na Kinsey dake Ilorin a jihar Kwara, Yakubu Ahmed, ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Ilorin bisa zarginsa da kashe abokinsa.
Wanda ake zargin da abokinsa Faruq Ahmed da Allah ya yi cikawa, an ce sun yi artabu da wukake, tare da jima juna ciwo gabanin rasuwarshi.
Rahoton ‘yan sanda na farko ya bayyana cewa, fadan ya faru ne sakamakon bacewar farantin abinci da mamacin ya aje.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, an garzaya da wanda ake tuhuma da wanda ya rasun zuwa asibitin koyarwa ta Jami’ar Ilorin (UITH) domin yi musu magani, amma daga baya Ahmed ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a lokacin da suke fafatawar.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun Adebayo Kudus, ya ce zai iya sauraron karar ne kawai, ammma kotunsa ba ta da hurumin sauraren karar.
Daganan sai ya bada umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhumar a gidan gyaran hali, sannan ya dage ci gaba da sauraren shari’ar har zuwa ranar 21 ga Maris, 2022.
