September 18, 2026

Gwamnatin Da Ta Tace Kowa Ya Kare Kansa Kuma Ita Ce Zata Haramta Ayyukan ‘Yan Sa Kai: Martanin CSOs Ga Gwamnatin Jihar Katsina

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Gammayar Kungiyoyin farar Hula a jihar Katsina sun bayyana matsayarsu akan sabon matakin da gwamnatin jihar Katsina ta dauka da Haramta duk wani aiki na ‘yan sa kai da kuma ‘yan banga a fadin jihar Katsina.

Wannan matsayar dai na zuwa ne kasa da awa 24 da gwamnatin jihar ta bada sanarwar ta bakin mai baiwa gwamna shawara akan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina ta fiitar ga manema labarai a Katsina.

Inda ta ce ta Haramta duk wani aiki na’yan sa kai da kuma bangaran yan Banda a fadin jihar Katsina domin karfafa harkon tsaro da ake fama da ita.

Sai dai kuma a nata bangaran gammayar kungiyoyin farar hula ta fitar da tata sanarwar wanda shugaban Ƙungiyar Abdulrahaman Abdullahi Dutsinma ya sanyawa hannu inda ta jefa wasu tambayoyi ga gwamnatin jihar Katsina gama da wannan mataki da ta dauka.

“me yasa gwamnati ke kokorin maida hannun agogo baya ta hanyar fada da sha’anin tsaro? Me yasa wannan ke zuwa daga gwamnatin da ta fito a bainar nasi ta ce kowa ya kare kansa? Ko ko dai yanzu ta samu isasun jami’an tsaron da su tabbatar da tsaro a jihar Katsina? In ji kungiyar

Sanarwa ta ce hatta ‘yan banga 500 da aka dauka aikin bayan anyi masu horo watanni bakwai da suka wuce an kasa biyansu hakkokinsu da tafiyar da su tare da sama musu kayayyakin aiki.

A maimakon Haramta ayyukan ‘yan sa kai da ‘yan banga da gwamnati ta yi kamata ya yi gwamnati ta lalubu hanyar da zata Inganta ayyukansu a zamanance. In ji kungiyar

Sanarwar ta cigaba da cewa a wannan lokaci da mutuwar jami’an tsaro ta zama ruwan dare gama duniya ‘yan sa kai na da rawar da za su taka wajan daidaita al’amurran tsaro a wannan jiha ta Katsina

“Akwai abubuwa da dama da ya kamata ace an tabbatar da wanzuwarsu ta hanyar kula da ayyuka wanda ke bukatar sa ido so sai, amma a irin wannan yanayi da gwamnati ta kasa wajan kare rayuwaka da dukiyoyin ‘yan jiha sannan take karfafa jama’a da su kare kansu ba tare da wata ka’ida ba, sai ace an haramta irin wadanda ayyuka’ inji sanarwar

Daga karshe sanarwar cewa ta yi ya kamata gwamnati ta nuna damuwarta so sai ta hanyar kawo karshen ayyunkan ‘yan bindiga da sauran manyan laifufuka a jihar Katsina kafin daukar irin wannan matakin saboda Hakan zai raunana jama’a wajan taimakawa gwamnatin ta kawo karshen wannan matsala.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *