November 17, 2026

Me Yasa Ba a Ganin ‘Yan Biyun Kannywood a tafiyar kungiyar Triple R?

IMG-20261026-WA0006

 

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Duk da kusancin da ke tsakanin Mawaki Dauda Kahutu Rarara da ‘yan biyun Kannywood Hassana da Hussaina Musa an gaza ganin su a tafiyar kungiyar Triple R Kannywood wadda shi Rarara din yake jagoranta.

 

Domin a baya sun yi ayyuka da dama tare musamman fitowa a cikin wakokin sa. Amma dai da tafiyar kungiyar Triple R Kannywood ta zo an ga Mata ‘yan Kannywood da yawa waɗanda ba su kai shi kusanci da su ba suna gaba gaba a tafiyar.

 

Kuma ko a baya da ba tafiyar siyasar su ɗaya ba suna aiki tare. A lokacin da suna Kwankwasiyya, shi kuma yana ɓangaren Ganduje.

 

Amma a yanzu da suka biyo Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC a maimakon a gan su tare a tafiyar kungiyar Triple R Kannywood, sai aka ga babu su.

 

Ko da muka tambayi Hussaina Musa a game da rashin ganin na su a kungiyar Triple R cewa ta yi “gaskiya da mu aka fara tafiyar kungiyar Triple R Kannywood, daga baya ne dai muka ja baya, kuma shi ma Rarara bai so hakan ba. Don ya yi ta kiran mu da mu zo a yi tafiyar da mu, amma dai ba mu je mun ci gaba da tafiyar ba.

 

Amma hakan ba ya nuna ba mu da alaƙa da shi ba ne kawai dai ba ma cikin kungiyar Triple R ne. Kuma rashin ganin mu a tafiyar, wani al’mari ne na kashin kan mu”. Inji Hassana Musa.

About The Author