CDP TA SHIRYA TANTANCE AYYUKAN DA TA AIWATAR A ƘANANAN HUKUMOMIN KATSINA
Shirin Bunƙasa Al’umma na Jihar Katsina-CDP, ya ce yana shirin gudanar da aikin sa ido da tantance dukkan ayyukan da shirin ya aiwatar a ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Shugaban shirin na CDP na jihar Katsina, Associate Professor Kamaladdeen Kabir, ne ya bayyana haka yayin wani taro da jami’an sa ido da tantance ayyuka na shirin.
Wata sanarwar manema labarai da Jami’in Hulɗa da Jama’a na shirin, Ashiru Mamman Ingawa, ya fitar, ta ambato Associate Professor Kamaladdeen Kabir yana cewa za a gudanar da aikin tantancewar ne a matakai daban-daban.
Ya ce za a fara da bincike da tantance babura da aka bai wa wasu masu ruwa da tsaki da ke aiwatar da ayyukan CDP a sassa daban-daban na jihar.
Shugaban shirin na CDP ya ce manufar tantancewar ita ce tabbatar da cewa baburan da aka bai wa masu ruwa da tsakin su ne waɗanda aka samar musu, tare da tabbatar da cewa ana amfani da su yadda ya kamata.
Ya umarci jami’an sa idon da tantance ayyukan da su duba bayanan baburan a yayin aikin, tare da kai rahoton duk wani abu da ba daidai ba domin ɗaukar matakin da ya dace.
Haka nan kuma, Associate Professor Kamaladdeen Kabir ya buƙaci masu ruwa da tsaki na shirin na CDP da aka bai wa baburan da su ba jami’an sa ido da tantance ayyukan cikakken haɗin kai da goyon baya yayin gudanar da aikin.
Da yake maida jawabi, Manajan Sashen Sa Ido da Tantance Ayyuka, Malam Kabir Sirajo, ya ce za su gudanar da aikin ne bisa ƙa’idoji da sharuɗɗan da aka gindaya musu.
Malam Kabir Sirajo ya tabbatar wa shugaban shirin na CDP cewa za su sauke nauyin da aka ɗora musu ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.
