September 16, 2026

Gwamna Raɗɗ ya yi alƙawarin tsara Cigaban Jihar Katsina Bisa Ingantattun Bayanai

IMG-20260711-WA0021

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tara cikin jihar a bisa sahihan bayanan da suka haɗa da yawan jama’a da samar da ayyukan yi.

 

Ya ƙara da cewa zai tabbatar da kyautata kiwon yada ilmi da muhimman ababen more rayuwa ga al’ummar jihar Katsina.

 

Wannan yana cikin wani sako na bikin ranar yawan al’umma duniya ta shekarar 2026 inda gwamnan ya bayyana cewa karuwar jama’a na tattare da kalubale da damarmaki na cigaba.

 

Yana mai cewa gwamnatin jihar Katsina za ta ƙarfafa tattara sahihan bayanai da faɗaɗa ayyukan tsara iyali da koyar da matasa sana’o’i da kwarewa tare da samar da yanayi mai kyau

 

Kazalika gwamna Raɗɗa ya umarci dukkan ma’aikatu da hukumomi da sassan gwamnatin jihar Katsina da su tsara ayyukan su na shekarar 2026 bisa sabbin bayanan yawan jama’a.

 

Ya ƙara da cewa da cikin abubuwan da za su baiwa fifiko sun haɗa da kiwon lafiyar mata da yara da ilmin ‘ya ‘ya mata da tabbatar da wadataccen abinci tare da yin kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin kungiyoyin Addinai da na fararar huka da kuma na yaɗa yau hada kai da gwamnati wajen wayar da kan jama’a kan mahimmancin tsara iyali da yin rijistar haihuwa

 

Haka kuma gwamna Raɗɗa ya taya wakilin jihar Katsina a hukumar kididdiga ta ƙasa Ferfesa Sadiq Isah Raɗɗa murnar rantsar da shi a matsayin Kwamishina da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi

 

Daga ƙarshe Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana ƙwarin gwiwar da akan Ferfesa Sadiq Isah Raɗɗa bisa gogewarsa wajen tabbatar da cewa jihar Katsina ta samu cikakken wakilci da samun sahihan bayanai a matakin ƙasa

About The Author