Tsaftace Muhalli: Akwai Abubuwan Koyi ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Dutsinma. -Kwaramad Mannir Suleiman
An kira ga shugaban ƙaramar ƙungiyar Funtua Hon. Abdulmutalib Goya da ya yi koyi da takwaransa na Dutsinma wajen aikin tsaftace muhalli.
Wannan kiran ya fito ne da shugaban gidauniyar hadin kan jama’ar Funtua Kwamarad Mannir Suleiman a lokacin tattaunawar da da manema labarai
Kwamarad Mannir Suleiman ya ce ya nuna buƙatar da ake da ita ga shugaban ƙaramar hukumar Funtua da ya yi koyi da na Dutsinma wajen aiwatar da kyakkyawar ayyuka.
A cewar sa, yin haka zai taimaka wajen rage cututtukan masu yaɗuwa da marasa yaɗuwa a tsakanin al’umma, kuma hakan zai taimaka wajen kawar da cutar maleriya baƙi ɗayan ta
Kwamarad Mannir Suleiman ya karfafa cewa haɗa gwaiwa da sashen kula da tsaftace muhalli na ƙaramar hukuma zai taimaka maka matuƙa gaya
Ita ma gidauniyar hadin kai yankin Funtua zata kasance wajen haɗa hannu domin tsaftace muhalli a garin Funtua.
Ya ce suna fatan shugabancin gidauniyar zai ɗauki mataki kamar yadda sauran ƙananan hukumomi suka rigar suka yi nisa wajen tsaftace muhalli.