Yadda Kungiyar Inuwar Daliban Arewa Ta Karrama Dakta Askiya Sheikh Nasiru Kabara
Yadda Kungiyar Inuwar Daliban Arewa Ta Karrama Dakta Askiya Sheikh Nasiru Kabara
DAGA MUKHTAR YAKUBU
Kungiyar Inuwar Daliban Arewa wato Arewa Student From ta karrama fitaccen Malamin Addinin Muslumci kuma shugaban kungiyar Al’umma masu bukatar kawo sauyi ta kasa wato NCPC da Lambar girmamawa a matsayin sa na guda daga cikin muhimman mutane a kasa da suke bayar da gudummawar su ga Al’umma musamman ta bangaren Dalibai da kuma ci gaban karatu.
A lokacin bayar da kambun karramawar da aka gudanar a ofishin sa da ke kan titin Zaria a ranar Juma’a 22 ga Agusta 2025.
Da yake bayani dangane da dalilin zuwan na su har ofishin Malamin domin Karrama shi shugaban kungiyar Inuwar Daliban Arewar ya bayyana cewar.” Sun yi wannan karramawar ne bisa bincike da suka yi na ayyukan Malamin da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban Ilimi tun daga matakin farko har zuwa manyan makarantu don haka suka ga ya kamata su karrama shi domin ƙara masa karfin gwiwa wajen gudanar da ayyukan sa na taimakon al’umma
Ya kara da cewa ” Babu shakka Dakta Askiya Sheikh Muhammad Nasiru Kabara ya cancanta a karrama shi domin ta kowanne fage yana bayar da gudummawar sa ga ci gaban al’umma, walau ta ɓangaren karatu ciyarwa ga masu bukata da taimakon raunana.
Don haka a kullum wannan kungiyar tamu take bincike domin gano irin sa don a Karrama su yadda za su samu karfin gwiwa wajen ci gaba da ayyukan da suke yi.”
Shi ma da yake mayar da Jawabi bayan karrama shi da aka yi. Doka Askiya Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, ya nuna matukar farin cikin sa da karramawar da ɗaliban suka yi masa wanda a cewar sa wannan wata manuniya ce da take tabbatar da cewa abubuwan da muke yi na taimakon al’umma mutane suna amfana har ma da ta kai wasu daga nesa suka ga abin da muke yi suka zo don su Karrama mu.
Ya ci gaba da cewa ” Duk da ba wannan ba ne farko da kungiyoyi da Hukuma da kuma daidaikun mutane suka fara karrama mu, to Amma wannan abin alfahari ne a ce kungiyar Inuwar Daliban Arewa sun bamu wannan kambu na karrama.
Ina godiya a gare su da sauran Al’umma da suke bada gudummawa tare da masu karfafawa masu bayar da gudummawa kamar dai wannan kungiyar ta Daliban Arewa”.
Daga ƙarshe Malamin ya yi kira ga ɗaliban da ma sauran al’umma da su mayar da hankali wajen samar wa matasa hanyoyin dogaro da kai da kuma ba su tallafin karatu.
