Yan Bindiga Sun Ƙaƙabawa Manoma Harajin Miliyan 15 Kafin A Barsu Su yi Noma -Wani Kansila
‘Yan Bindiga Sun Ƙaƙabawa Manoma Harajin Miliyan 15 Kafin A Barsu Su yi Noma -Wani Kansila
Kansila Mai wakiltar mazaɓar Na Alma a ƙaramar hukumar Malumfashi Hon. Usman A. Usman ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun ƙaƙaba masu haraji har na naira miliyan 15 idan suna so a bar su su yi noma.
Kansilan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Leadership a Malumfashi inda ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun ce mutanen mazaɓar Na Alma zamu biya harajin miliyan 10 tare da sayo wasu kayayyaki da suke kai miliyan 5
Hon. Usman A. Usman ya bayyana yawaitar kashe-kashen jama’a a ƙaramar hukumar Malumfashi a matsayin abin takaice inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi wani abu don ganin an magance wannan matsala.
A cewar sa, idan har mutanen da yake wakilta suna san zuwa gonakin su dole sai an biya wancen haraji da aka ƙakaba masu na naira miliyan 15 Kafin su je gonakin su a wasu keɓaɓun lokuta da aka ware masu.
Kazalika Hon. Usman ya nuna damuwa akan yawaitar kashe-kashen jama’a da ya zama ruwan dare gama duniya a ƙaramar hukumar Malumfashi inda ‘yan bindiga ke kewaye da al’ummomi suna kashe su da sace su tare ƙaƙaba masu haraji
” Yanzu abinda suke buƙata daga wajen mu shi ne, naira miliyan 10 da kuma mashina guda biyu korar Honda wannan lamari dai ya shafi aƙalla garuruwa tara a mazaɓar Na Alma a ƙaramar hukumar Malumfashi” inji shi.
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun bayyana masu cewa idan aka biya wancan buƙata ta su, to Manoma za su riƙa zuwa gonakin su daga karfe takwas na safe zuwa karfe ɗaya na rana
Hon. Usman ya ce wannan shine sharaɗin da ‘yan bindigar suka gindaya masu idan har sun cika wancan alƙawarin na su cigaba da zuwa gonakin su ba tare da kai masu hari ba, kubba wanda ya isa ya kaucewa wannan sharaɗi
Ya kara da cewa an fara haɗa waɗannan kuɗaɗai inda kowane magidanci zai biya naira dubu goma duk da cewar maharan ba su daina kai hari ba.
Kansilan dai ya bayyana cewa zuwa yanzu kimanin al’ummomi 16 ne suka yi hijira daga garuruwan su da gonakin su zuwa manyan garuruwan kamar irin su Dayi da Malumfashi domin tsira da ransu
