AGILE : A Zamfara Ta Kaddamar Da Kulab Na Dalibai Akan Amfani Da Dashen Itatuwa Da Tsafatace Muhalli
AGILE : A Zamfara Ta Kaddamar Da Kulab Na Dalibai Akan Amfani Da Dashen Itatuwa Da Tsafatace Muhall
Daga Hussaini Yero
Cibiyar (AGILE) ta Kaddamar da Kulab na dalibai a makarantun Sakatare Mata a Zamfara dan horar dasu akan tsaftace Muhalli da Dashen Itatuwa,da kuma kula da Sabbin gine gine da AGILE tayi a cikin makarantun da kuma yadda abokan karatunsu da suka daina zuw makarata zasu dawo su cigaba da zuwa makarata.
Makarantun da suka amfana sun hada da Manyan Makarantun Sakandare da aka soma daga Zurmi, Shinkafi, Kauran Namoda Anda Birnin Magaji a karamar hukumar Zurmi.
Da yake jawabi a lokacin kaddamar da kungiyoyin makarantun Zamfara AGILE, mai gudanar da aikin, Ishaka Idris Maikwai, ya ce horon yana da manufa guda biyu wanda ya fi mayar da hankali kan wayar da kan muhalli, ilimin dijital, dabarun rayuwa da matakan rigakafin cin zarafi.
A cewar Maikwai dalibai na bukatar wayar da kan su kan yadda za su yi amfani da kansu wajen zubar da shara wanda a karshe za a iya sarrafa su don inganta tattalin arzikinsu don samun ingantacciyar rayuwa a lokacin karatun sakandare.
“Akwai abubuwa da yawa da ake amfana da sharar idan akatarata a gida ,ana kaita gona dan samun amfani mai yawa kuma ana kasuwanci da ita asaida idan Daliban ta saida zata taimaka mata wajan dogaro da kai wajen magance buƙatun nan take.
“A wani bangaren kuma,yin shara akai akai yana inganta lafiya ,da kauce ma kamuwa da zazabin cizon sauro da kuma samun ingantaciyar lafiya .inji Ishaka Maikwai.
Kuma ya jawo hankalin da daliban mata da imanin cewa za su iya rayuwa cikin walwala da annashuwa batare da cin zarafi ba,duk daliban da akaci ma zarafi su guji jin kunya wajen neman hakkinsu da tsarin mulkin kasar ya ba su, sannan su daina jin kunya da tsoron da bada rahoton faruwar al’amura ga hukumomin da abin ya shafa.
Maikwai ya sake nanata cewa, “Taron ya shafi jajircewar AGILE na wayar da kan jama’a game da wayar da kan muhalli, abubuwan da ke haifar da sauyin yanayi, illa da kuma mafita musamman dashen itatuwa da sarrafa shi a cikin makarantu.
“An kuma umurce ku da ku kiyaye kayayyakin more rayuwa (sababbin gine-gine da kuma gyaran fuska gami da WASH) ta hanyar kai rahoton barna ga hukumomin makarantu”, Ishaka Mai Kwai ya nemi.
