November 18, 2026

Hon. Aminu Balele Ɗan Arewa Ya jagoranci addu’a Ta Musamman Ga Marigayi Hajiya Safara’u Umar Bare-bari 

IMG-20250323-WA0007

Hon. Aminu Balele Ɗan Arewa Ya jagoranci addu’a Ta Musamman Ga Marigayi Hajiya Safara’u Umar Bare-bari

Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kurfi da Dutsinma, Alhaji Aminu Balele Dan arewa, ya jagoranci gagarumin taro na yiwa marigayiya Hajiya Safara’u Umar Bare -Bare, Mahaifiyar gwamnan Katsina addu’ar Allah ya kara mata Rahama da ni’ima.

Anyi gagarumin taron a babban dakin taro na jami’ar, FUDMA dake garin Dutsinma.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙananan hukumomin Dutsinma da kurfi da kansilolin su dukkanin shugabannin jami ‘iyyar APC tun daga mazaba zuwa karamar hukuma.

Taron ya kuma samu halartar limamai da Malamai daga kananan hukumomin Dutsinma da Kurfi.

Taron ya kuma samu halartar mataimakiyar shugaban jami’ar FUDMA da wasu manyan mukaraban da suka halarta.

Bayan kammala taron Dan majalisan tarayyar ya gwangwaje matasa da kwamfutoci domin sana’a.ya kuma ba wakilan jam’iyyar da suka halarta da kyautar Naira miliyan goma suka raba a tsakaninsu.

Anyi taron lafiya an tashi lafiya

About The Author