Yan Sanda Sun Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Kaiwa Yan Bindiga Kakin Sojoji A Katsina
Rundunar ‘Yan Sanda ta yi nasarar damke wasu mutane huɗu da ake zargin suna kaiwa ‘yan ta’adda kakin sojoji domin cigaba da ayyukan ta’adanci a jihar Katsina.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ASP Abubakar Sadiq ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Katsina
ASP Abubakar Sadiq ya ce sun samu nasarar kama wani Aminu Hassan ɗan shekaru 25 da ke garin Dundubus a ƙaramar hukumar Danja ta jihar Katsina wanda ake zargin sa da ɗaukar nauyin ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Ɗanmusa.
Ya ƙara da cewa sun kama wanda ake zargin ne a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2024 akan hanyar Yantumaki zuwa Kankara da kayan sojojin Nijeriya acikin wata jikka.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, lokacin da suke gudanar da bincike sun kama wasu ƙarin wasu mutane uku da suka haɗa da Lawal M Ahmad mai shekaru 29 da Isma’il Ɗalhatu ɗan shekara 24 dukkan su suna zaune ne a garin Basawa ta Sabon Gari Zaria a jihar Kaduna.
Sannan akwai Shafi’u Adamu ɗan shekara 28 da ke zaune a kauyen Danjaba a ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna dukkan su suna da alaƙa da wancan tuhuma ta kakin sojoji 14 da kuma na ɗan Sanda guda ɗaya wanda ake zargin za su kaiwa ‘yan bindiga domin tada zaune tsaye.
Sanarwar ta ce lokacin da jami’an ‘yan sanda ke gudanar da bincike waɗanda ake zargin sun tabbatar da aikata wannan laifi da ake zargin su da aikatawa, kuma da zaran an kammala bincike za a miƙa su gaban kuliya manta sabo.
Daga ƙarshe sanarwar ta ruwaito kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina CP Aliyu Abubakar Musa yana ƙara kira ga al’umma da su cigaba da taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri da za su taimaka wajen dakile ayyukan ‘yan ta’adda a jihar Katsina baƙi ɗaya
