September 18, 2026

Burin Tinubu shi ne kowanne ɗan Nijeriya ya daina kwana da yunwa

FB_IMG_1733814193385

Burin Tinubu shi ne kowanne ɗan Nijeriya ya daina kwana da yunwa

Ƙaramin Ministan Noma, Aliyu Abdullahi, ya baiyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya duƙufa ne wajen tabbatar da cewa abinci ya wadaci ƴan Nijeriya.

Da ya ke magana a shirin Sunrise Daily na Channels TV a yau Litinin, Abdullahi ya ce burin Tinubu shi ne ya tabbatar da cewa ko wanne ɗan Nijeriya ya kwanta barci a ƙoshe.

Ya ce shi ya sa gwamnatin Tinubu ke kirkiro da shirye-shirye daban-daban don tabbatar da wannan ƙudiri na shugaban ƙasa.

Daily Nigeria Hausa

About The Author