September 18, 2026

Malaman Firamare Dubu 17,000 Sun Samu Horo A Fanni Daban-daban a Katsina.

0

Malaman Firamare Dubu 17,000 Sun Samu Horo A Fanni Daban-daban a Katsina.

Hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar Katsina ta bayyana cewa a cikin shekara guda, an horas da malaman firamare dubu sha bakwai daga cikin dubu talatin da ake da su a fadin jihar Katsina.

Shugaban hukumar Dakta Kabir Magaji ne ya bayyana haka a lokacin taron manema a Katsina.

Dakta Kabir Magaji ya ƙara da cewa daga watan Yuni na shekarar 2023 zuwa watan Satumba 2024 fiye da malamai dubu sha bakwai suka samu horo a ƙoƙarin gwamantin na inganta koyo da koyarwa.

A cewar sa, baiwa malaman horon ya zama wajibi ganin irin yadda ake samun ƙaruwar ɗalibai wanda yanzu haka, akwai kimanin ɗalibai miliyan biyu da dubu ɗari takwas da hamsin da biyar a faɗin jihar Katsina (2, 8550:00)

“Haka kuma gwamnatin jihar Katsina ta kashe kuɗi kimanin naira miliyan 68 wajen ɗaukar nauyin ɗalibai zuwa gasa a ƙasahen waje da kuma cikin gida Nijeriya.” Inji shi

Dakta Kabir Magaji ya ƙara da cewa suna fuskantar kalubalen yawan ɗaliban a makarantun firamare wanda ya ce sun shirya kawo karshen wannan matsala ta hanyar samar da karin ajujuwa a faɗin jihar Katsina.

Shugaban hukumar ya cigaba da cewa zuwa yanzu hukumar su, ta kashe kimanin naira biliyan 15 wajen fadadawa da inganta harkokin ilmi a jihar Katsina.

Kazalika hukumar ilimin bai ɗaya ta kashe naira miliyan 22,500,000 wajen sayen allonan karatu da dasta domin rabawa a makarantun firamare na jihar Katsina.

Daga ƙarshe, Dakta Kabir Magaji ya ce a cikin shekara ɗaya da zamansa shugaban hukumar ilmin bai ɗaya ta samu nasarorin guda 72 wanda ya ce hakan ya samu ne a dalilin muhimmanci da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya baiwa harkar ilimi a jihar Katsina

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *