September 18, 2026

Shinkafa Buhu 7,200 Da Ake Zargin An Karkatar A Katsina Ta Minista Dangiwa Da Kungiyar Izala Ce -Gwamnatin Jihar Katsina

0

Shinkafa Buhu 7,200 Da Ake Zargin An Karkatar A Katsina Ta Minista Dangiwa Da Kungiyar Izala Ce -Gwamnatin Jihar Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa shinkafar da jami’an tsaro na DSS suka kama buhu 7,200 a wasu shagunan ajiye abinci a babbar kasuwa ta Fatima Baika ba ta gwamnatin jiha ba ce.

Babban sakatare na gwamnan jihar Katsina Abdullahi Aliyu Turaji ya bayyana haka ga menama labarai a Katsina.

Hon. Abdullahi Aliyu Turaji ya ƙara da cewa shinkafa ce bugu 1, 200 gwamnatin tarayya ta baiwa ministan gidaje da raya birane Ahmad Musa Dangiwa sai kuma kungiyar Izala ta jihar Katsina aka ba su buhu dubu 6,000 domin su rabawa jama’ar su.

Ya kuma ƙara da cewa abinda gwamantin jihar Katsina har ta shiga cikin maganar saboda jami’in ta da aka sanyi ciki wato mai taimakawa gwaman akan ayyukan more rayuwa Nasiru Lawal Kankia.

“Shi wannan mai taimakawa gwamna akan ayyukan more rayuwa ya gaya mana cewa Minista Ahmad Musa Dangiwa shi ya bashi wannan shinkafa domin a rabawa jama’a shi kuma ya Kaita wajen ajiye kayayyaki a manyan shagunan kasuwa” inji Turaji.

A jiya laraba ne jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun cika hannu da wasu ‘yan kasuwa da ake zargi da sayar da shinkafar da gwamnatin tarayya ta baiwa jihaho domin a rabawa talakawa a Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron farin kaya na DSS sun kai samamaye ne a babar kasuwa da ke Katsina a daren jiya laraba.

An dai rufe shaguna guda biyu da ake zargin an jibge shinkafar kimanin buhu dubu biyu wanda yanzu haka jami’an tsaron sun kwasheta zuwa ofishin su.

Gamayyar Kungiyoyin farar hula a jihar Katsina sun yi Allah wadai da faruwar wannan lamari tare da nuna takaicin yadda aka karkatar da wannan shinkafa da gwamnatin tarayya ta bada domin a rabawa talakawa.

Shugaban kungiyar AbdulRahman Abdullahi Dutsinma ya ce sun zuba Ido suga abinda gwamnatin jihar Katsina zata akan wannan lamari wanda ya kira da abin baƙin ciki da takaici.

Ya ƙara da cewa dalilin raba wannan shinkafa shine domin a rabawa talakawa da suke fama da matsanancin rashin abinci, amma an samu wasu marasa kishi sun karkatar da ita.

Wani ɗan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina Suke Dudu kofar Marasa ya ce wannan ba abin mamaki bane a gwamantin APC, ya ce suna iya yin abinda ya fi haka ma.

A cewar sa lokacin zuwan wannan gwamnati har wata hukuma ta cin hanci da rashawa, ya ce yanzu ne ya kamata aga aikin ta yadda ya kamata.

Yanzu dai kowa ya zuba Ido ya ga irin matakin da gwamnatoci za su ɗauka akan faruwar wannan lamari mai cike da ban mamaki da takaici.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *