September 18, 2026

Sarkin Katsina Ya Jinjinawa Tunibu Akan Bada Aikin Hanyar Mararaba Zuwa Katsina.

0

Sarkin Katsina Ya Jinjinawa Tunibu Akan Bada Aikin Hanyar Mararaba Zuwa Katsina.

Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya jinjinawa shugaba Bola Ahmad Tunibu akan bada aikin hanyar da ta ta so daga marabar Kankara zuwa zuwa cikin birnin Katsina.

Sarkin ya yi wannan jinjina ne a lokacin da ‘yan kwangilar suka kawo masa ziyarar ban girma da sanar da shi wannan gagarumin aiki wanda suka ce zai lakume biliyoyin nairori.

Idan za a iya tunawa wannan hanya a sake yin ta a shekarar 1997 wanda yanzu haka ta koma wani sansani na haddasa haɗura da ɗaukar rai

Mai Martaba Sarkin ya nuna mahimmancin sake gina wannan hanya inda ya ce lallai zata taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da zirga-zirga a wannan yanki musamman da saboda manoma da sauran al’amuran rayuwa.

Haka kuma Sarkin Katsina ya koka game da hanyar da ta taso daga Kano zuwa Katsina wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya bada aikin ta, amma har yanzu ko rabi ja a yi shekaru bakwai da bada aikin hanyar.

“Na yi magana har na gaji akan hanyar Kano, amma shiru, ba zan daina magana ba akan wannan hanya ba saboda mahimmancin ta a cikin al’umma, saboda mahimmancin hanya har Masallaci ana rushewa domin ayi ta” inji Mai martaba Sarki

Sarkin ya yi kira ga ‘yan kwangilar da su yi aiki mai nagarta wanda za a yaba ma su ko bayan sun kammala aikin sun tafi, ya kuma ba su tabbacin goyon baya daga masarauta a duk lokacin da suke buƙatar hakan.

Shima da yake jawabin dalilin kawo ziyarar shugaban kamfanin Vipan Construction limited Mista Marun wanda aka baiwa aikin wannan hanya mai tsawon kilo mita 170 Ya bayyana cewa sun zo faɗa ne domin neman albarka wajen uban al’umma mai martaba Sarki.

Ya ƙara da cewa, za su aiki tsakanin su da Allah kamar yadda aka kulla yarjejeniyar aikin da su, kuma za su tabbatar an yi aikin cikin lokaci da aka kulla yarjejeniya da su wato shekara biyu

Mista Marun ya bada tabbacin cewa shugaba Bola Ahmad Tunibu ya bada wannan aiki a wasu jihohin arewa ciki harda jihar Katsina domin kawo cigaba a wannan yanki.

Al’ummomi da dama da muka zanta da su akan wannan cigaba sun bayyana jin dadin su game da aikin hanya musamman yadda aka baiwa matasan su aiki fiye da mutum dubu ɗaya.

Haka kuma sun nuna fatan cewa za a kammala wannan aiki daidai lokacin da aka bayyana za a kammala wato shekara biyu daidai.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *