Gwamnan Jihar Katsina Ya Buƙaci Tsaffin Ɗaliban Kwalejin Ilimi Ta Kafanchan Da Su Taimaka Ma Cigaban Ilimi.
Gwamnan Jihar Katsina Ya Buƙaci Tsaffin Ɗaliban Kwalejin Ilimi Ta Kafanchan Da Su Taimaka Ma Cigaban Ilimi.
Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya buƙaci tsaffin ɗaliban kwalejin ilimi ta Kafanchan da su haɗa kansu wajen taimaka ma ci-gaban ilimi a kowane mataki.
Hakan nada nufin dawowa da martabar ilimi a makarantun gwamnati domin samun al’umma mai ilimi da za a yi alfahari da ita.
Radda ya yi wannan rokon ne kafin amsar lambar karramawa a wajen wani taron walima na masamman da bada lambar karramawa domin girmama shugaban ma’aikata da sauran ɗaliban da suka kammala karatun a shekarar 1987 a kwalejin wanda ya gudana a dakin taron sakatariyar jihar Katsina.
Gwamnan ya ce dukkansu sun yi karatu a makarantun gwamnati lokacin da akwai kwararrun malamai da kayan aiki.
Gwamnan ya bayyana jindadin ta yadda ɗaliban makarantar suka mamaye manyan mukamai a gwamnati, da ya haɗa da shi kanshi, mataimakin gwamna, shugaban ma’aikata na gidan gwamanti, shugaban ma’aikatan jiha, da dai sauransu.
A nashi ɓangaren, shugaban ƙungiyar tsaffin ɗaliban Umar Dangi Abas ya ce shugabannin ƙungiyar na riƙon ƙwarya sun yanke shawarar gudanar da zaɓe domin ba wasu ƙarin mutanen damar shiga cikin shuagabancin ƙungiyar.
A daidai lokacin da yake yaba ma gwamnan jihar bisa naɗa wasu tsaffin ɗaliban makarantar a manyan mukamai na shugabanci, Umar Dangi ya sanar da tsare-tsaren shirya taro a matakin ƙasa domin girmama gwamnan jihar a cikin watan Janairun shekara mai zuwa.
A saƙonshi na godiya, shugaban ma’aikata Falalu Bawale ya bayyana ƙoƙarin da gwamna ya yi wajen sake fasalin ilimin jihar nan a cikin shekara ɗaya.
Sauran da aka ba lambar karramawar sun haɗa da mataimakin gwamnan jihar Katsina Faruq Lawal Jobe, shugaban ma’aikata Falalu Bawale, Dr. Abdulmalik Durugunwa da kuma Barrister Murtala Aliyu Kankia.
