September 18, 2026

Bikin Sallah: Yadda Wanban Faskari Ya Tallafawa Kungiyoyii Da Kayan Abinci Da Kuɗaɗe A Katsina

0

Bikin Sallah: Yadda Wanban Faskari Ya Tallafawa Kungiyoyii Da Kayan Abinci Da Kuɗaɗe A Katsina

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Katsina Hon. Hamza Suleiman Faskari (Wanban Faskari) ya tallafawa kungiyoyi da dama domin gudunar da hidimomin Babbar Sallah.

Taimakon wanda ya haɗa da masu buƙata ta musamman ‘yan gudun hijira da ‘yan jarida an yi shi ne domin rage raɗaɗin da ake fama da shi na tsadar rayuwa da kayan masarufi a ƙasa baƙi ɗaya.

Daga cikin abubuwan da kwamishinan ya raba sun haɗa da; da kayan abinci da kuɗaɗe ga al’umma domin gudanar da hidimomin Babbar Sallah acikin yanayi mai dadi da walwala.

Wasu daga cikin ‘yan jaridu da suka yi magana, sun bayyana cewa babu shakka wannan tallafi zai taimaka wajen gudanar da hidimomin Sallah ba tare da sarkakiya ba.

Sannan suka ƙara da cewa daman can Hon. Hamza Suleiman Faskari abokin ‘yan jaridu ne, da suke yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shi wanda ya saba taimakawa idan buƙatar hakan ta taso a tsakanin ‘yan jaridu a jihar Katsina

Da yake zantawa da wasu daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tallafin, Hon. Hamza Suleiman Faskari ya ce Kazalika bada tallafin yana da alaƙa da irin kiyaye-kirayen da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa yake yi ga jami’an sa da su riƙa yin wani abu da zai taimakawa ƙoƙarin gwamantinsa domin rage raɗaɗin da ake fama da shi a ƙasa baƙi ɗaya.

Sannan ya ƙara nuna buƙatar da ake da ita na faɗaɗa wannan tallafi zuwa waɗanda bala’in ‘yan bindiga ya shafa a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar Katsina da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga

Kwamishinan ya jinjinawa gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa akan yadda yake tallafawa jama’a da abubuwan more rayuwa musamman marasa karfi a cikin al’umma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *